Rayuwar macen Bahaushe abun a tausaya mata ne.
Ga dalilai kamar haka:
1. Ta fiye kula da mijinta da nuna masa soyayya da kwalliya a gidan mijinta, musamman a ce gidan yawa ne sai a ce 'yar bariki ya auro.
Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint
2. Ta riƙe sana'a tana samun abun yau da kullum a ce karuwa ce ko mai zaman kanta ce.
3. Ta girma Ubangiji bai kawo mijin aure ba a ce ta yi kwantai ba ta da hali mai kyau.
4. Ta yi aure ta zauna da mijinta lafiya a ce malamai take bi da bokaye ta shanye shi.
5. Ta yi karatu tana aiki a ce yawon banza take zuwa da shashanci.
6. Tana zaune da dangin miji lafiya a ce munafuka ce.
7. Ta yi magana a kan haƙƙinta a ce ba ta da haƙuri ko masifaffiya ce .
8. Ta yi aure ta fito a zageta a ce ta ƙi zaman aure koda kuwa mijin yana dukanta da cin zarafinta ne.
9. Ta fiye faran-faran da maƙota da sauran mutanen unguwa a ce shashasha ce .
10. Ta yawaita jan girmanta da dattaku a ce ba ta da kirki, ba ta da mutunci .
Allah ya ganar da mu gaskiya Amin.