Friday, 3 January 2025

Abubuwa 10 Ba Ku Buƙatar Su A Sabuwar Shekara

Tura Wannan Zuwa Ga

Waɗannan su ne abubuwan da ya kamata ka zubar da su a wannan sabuwar shekarar, kada ka ci-gaba da tafiya da su.


Ga su kamar haka:


1. Rabon ka ba ya tsere maka


Wanda ya tashi tsaye ya nema Allah zai taimake shi ya samu.


Abubuwa 10 Ba Ku Buƙatar Su A Sabuwar Shekara
Hoto: Window would

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


Wanda ya kwanta kuma sai abin da hali ya yi. Don haka ka tashi ka nema, kada ka jira lokaci.


2. Shugabanni ba sa son taimakon na ƙasa


A wannan ƙarnin da muke ciki shugabanni musamman irin na Nigeria ba ruwansu da kai, ko ka yi nasara ko akasin haka. Don haka ka tsara rayuwar ka cikin irin damar da kake da ita, ka kuma zage damtse wajen kyautata matsayin ka (Personal Development) ka nemi taimakon Allah (SWT).


3. Ƙoƙarin burge mutane


A mafi yawan lokuta abubuwan da kake yi domin burge jama'a kanka kawai kake burgewa. Wanda kake ba wa sha'awa ba ya buƙatar ka sauya komai game da kanka.


Wanda ba ka burgewa kuma kome ka yi ba za ka burge shi ba.


4. Kuɗi ba komai ba ne


Tabbas ba mu zo duniya domin neman kuɗi ba, sai dai da yawan abubuwan da muke buƙata domin mu rayu cikin mutunci da sanin ya kamata, talauci abokin gabar su ne.


Wadata tana sa mutum ya tsare mutuncin sa, ya kiyaye cin haram.


Wani lokaci hatta ibada ta fi tsayawa idan kana cikin hayyacin ka.


Don haka ka dage ka nemi kuɗi.


5. Raina sana'a


Har yanzu akwai waɗanda suke ganin sun fi ƙarfin wata sana'a saboda wasu dalilai nasu, amma fa ba su wuce maula da roƙo ba.


To ka sani yadda Nigeria ta ɗauki zafi yanzu, mai taimakon a baya, shi ma yanzu taimakon yake nema.


Don haka ka kama sana'a komai ƙanƙantar ta.


6. Zage-zage da shirme a shafukan sada zumunta 


Ka sani duk abin da kake yi a shafukan sada zumunta mutane suna kallon ka, kuma da yawa ba za su yi maka magana ba amma duk ranar da mu'amala ta haɗa ka da su, za ka karɓi sakamakon ayyukan ka a hannun su. 


Gwargwadon yadda ka nuna waye kai. Don haka ka saisaita mu'amalar ka a cikin wannan sabuwar shekara.


7. Wasa da alaƙa da raina mutane


Duk wanda ka haɗu da shi a rayuwa, ba ka san hikimar Ubangiji game da hakan ba.


Ta yiwu shi ne mai taimakon ka a rayuwa, kuma komai rashin matsayin sa.


Da yawan lokaci za ka raina matsayin mutum, kuma akwai sirri a tare da shi ko kuma ka kalli wani abu a tare da mutum, amma holoƙo ne, shi ma ta kansa yake yi.


Don haka ka girmama kowa, ko domin Allah (S.W.T) ya yi umarni da hakan.


7. Mummunan zato da yaɗa sharri


Kusan yana neman zama al'ada da zarar wani abu mara daɗi ya faru, sai ya zama abin yayi.


Kowa ya yi ta yaɗawa ba tare da tabbacin gaskiyar al'amarin ba.


Irin wannan ɗabi'a tana cutar da mai yin ta ba tare da ya sani ba.


Domin zaton ka yana shafar tunanin ka, kamar yadda tunanin ka yake zama aikin ka, da kuma makomar ka.


9. Kwaikwayo da yayi


Duk abin da ka ga wani yana yi ba ka san manufar sa akai ba.


Idan ka shiga kwaikwaya ba tare da ilimin abin ba, kana iya samun kanka a inda ba ka so.


Don haka kana iya kwaikwayo, amma inda ya dace da manufar ka.


10. Wasa da addu'a


Duk abin da ka saka a gaba, kada ka yi wasa da addu'a. Akwai abin da idon ka da hankalin ka suke gani, akwai abin da hangen ka ba zai je kansa ba.


Addu'a ce kaɗai za ta magance maka abin da ya fi ƙarfin tunani da hankalin ka.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user