Wednesday, 22 January 2025

Abubuwa 10 Masu Lalata Rayuwa Nan Take

Tura Wannan Zuwa Ga

1. Yawan gayawa mutane shirin ka na gaba, ya zama ba ka da sirri, kowanne shiri da kake yi na ci-gaban kasuwancinka ko rayuwarka ta yau da kullum sai ka kwashe ka gaya wa wani.


Abubuwa 10 Masu Lalata Rayuwa Nan Take
Hoto: Sing up genius

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


2. Kuɗin da ka sayi wayar hannunka ya fi jarinka na kasuwanci yawa.


3. Kasa cewa mutane a'a, ma'ana duk wata buƙata da wani ya kawo maka ko za ta cutar da kai ka kasa ce masa a'a. Ka koyi cewa mutane a'a akan abin da ka san za ka takurawa kanka idan ka yi.


4. Kasa jure sha'awa, kasa daure sha'awar jima'i ko sha'awe-sha'awe na wasu abubuwan tun daga wayoyin hannu, motoci, suturu masu tsada . Idan ka biye musu koyaushe za ka siyar da na hannunka arha ka ce za ka canja sabo.


5. Ci gaba da zama da macen da bakwa kwanciyar hankali.


Zaman aure da macen da babu kwanciyar hankali a zamantakewarku, hakan zai hana ka nutsuwa da sanyawa ƙwaƙwalwarka fargaba da rashin samun mallakar tunaninka gaba ɗaya.


6. Shafukan sada zumunta. Idan ya kasance ka zama mayen shafukan sada zumunta daga What'spp sai facebook sai ka gangara Tiktok ba ka mayar da hankalinka kan rayuwarka ta zahiri tabbas lokacinka zai ƙare a banza ba ka more shi yadda ya kamata ba. Ba ina magana ne akan masu samun kuɗi da harkar ba.


7. Son burge mutane


Ƙoƙarin burge mutane ba inda zai kai ka face komawa baya dan kuwa adadin dagewarka wajen burge mutane adadin dagewar da mutane za su yi wajen mayar da kai baya a rayuwa.


8. Kwashe jarinka na kasuwa don ƙoƙarin gina gida.


Kasuwa tana kawo kuɗi yayin da Gidan Zama baya kawo kuɗi, idan kana ta kwasar jarinka babu lissafi kana ƙoƙarin gina gida a hankali jarin zai zaizaye ya zama ka daina samun riba a kasuwancin saboda ƙarancin jari ko ka rasa jarin ma gabaɗaya a ƙarshe ƙila sai dai ka karyar da gidan da ka fara ginawa ka ƙara ɗora wani jarin wanda ko rabin naka na farko ba lallai ya kai ba.


9. Mayar da wajen kasuwancinka dandalin hira. Wannan yana matuƙar ba wa ɗan kasuwa matsala wato ya zama kowa ya mayar da shagonka ko wajen kasuwancinka shi ne dandalin hirar siyasa da musun addini da zuwa a zauna a huta. 


Mutane kala-kala ne akwai waɗanda da dama ko siyayya suka zo suka ga jama'a da yawa a wajen wucewa suke yi saboda ba sa son  taron jama'a. Akwai kuma wanda ido ne ba ya so, ba ya so ya ga kowa ya san abin da zai siya.


10. Shan kayan maye


Na ƙarshe kuma mai muhimmanci duk abin da za ka yi ya zama kana cikin hayyacinka shi ne za ka tsara gabanka ka gane kuskuren bayanka.


Yo ba ka cikin hayyacinka ya za ka gane ma a wacce duniyar kake Jupiter ko Mars?

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user