Wednesday, 1 January 2025

Abubuwa 11 Da Za Ku Fara Yi A Farkon Sabuwar Shekara

Tura Wannan Zuwa Ga

1. Mu yi nazarin 2024, nasarorin da muka samu, da kurakuran da muka yi.


2. Mu mayar da hankali sosai wajen fahimtar kurakuren da muka tafka, da nufin gano musabbabin su, da yadda za mu kaucewa maimaita su a 2025.


Abubuwa 11 Da Za Ku Fara Yi A Farkon Sabuwar Shekara
Hoto: Good housekeeping 

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


3. Mu yi duba sosai akan abubuwan da suka fi cinye mana lokaci, mu ware waɗanda ba sa amfanar da mu, domin maye gurbin su da ayyukan da suke tallafar rayuwar mu.


4. Mu yi nazarin alaƙar mu da jama'a da nufin ƙara kusantar mutane na ƙwarai musamman waɗanda za mu koyi wani abu daga gare su (Mentors). Mu zare jikin mu daga mutanen da za su iya gurɓata rayuwar mu ko daƙile ci-gaban mu.


5. Ga wanda iyayensa suke raye, mu ƙara kusantar su tare da ƙoƙarin ba su farin ciki, hakan babban dafa'i ne. Kuma zai ƙarawa rayuwar mu albarka.


6. Sakamakon canjin rayuwa da aka samu, dole ne mu binciki yanayin samun kuɗin mu, tare da duba hanyoyin da za mu inganta neman mu, ko ƙara wasu hanyoyin samun kuɗin shiga.


7. Dole ne mu yi watsi da ɗabi'ar nuna isa da ƙasaita mara dalili, mu daina raina kowacce sana'a, matsawar za ta kawo kuɗi na halak.


8. Mu mayar da hankalin mu kan ƙanana da matsakaitan sana'oi waɗanda al'umma ta fi buƙata, akwai sirri da kuɗi mai yawa ga wanda ya fahimci alfanun ƙananan sana'o'i na gama gari.


9. Wajibi ne kowa ya ƙirƙiri asusu na ajiya, ya kuma tabbatar yana ɓoye wani abu komai ƙanƙantar samun sa, saboda ɓacin rana da larurori na bagatatan.


10. Kada mu ji kunyar tattauna matsalolin mu da waɗanda suka dace domin neman shawara ko shiriya (Guidance) don fita ko kaucewa matsalolin da suka dame mu.


11. Mu dinga samun lokacin nishaɗi muna jingine wasu matsalolin ko damuwa domin inganta lafiyar ƙwaƙwalen mu da samawa zuciyoyin mu sauƙi.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user