Thursday, 2 January 2025

Abubuwa 6 Da Za Su Sa Ka Yi Arziki A Sabuwar Shekara

Tura Wannan Zuwa Ga

KAR KA YARDA DA TALAUCI!


Shekarar 2024 ta wuce, amma har yanzu tarin matsalolinka suna nan ba su tafi ba, kuma girma yana ƙaruwa a kanka, burika da nauye-nauye  suna ƙaruwa.


Abubuwa 6 Da Za Su Sa Ka Yi Arziki A Sabuwar Shekara
Hoto: Freepik

Marubuci:- Abubakar Abba


Kasancewarka a Nigeria musamman ta Arewa, ya gadar maka da wasu tarin ƙalubale wanda ba a yi shawara da kai ba, da wasu matsaloli wanda ba ka shirya musu ba, da ƙarin wasu nauye-nauyen da al'umma da iyalai suka ɗaura maka wanda ya zama dole idan kana son zaman lafiya ko kana son ka tsira da mutumcinka, to ka yi ƙoƙarin ɗauka koda kuwa ba ka da ƙarfi.


Duk wata hanyar nasara da fita daga ƙangin talauci an saka mata shinge tun kafin ka zo duniya, hakan ta sa ya zama dole ka yi aiki tuƙuru ko kuma kai ma ka zama tamkar ragowar mutanenka.


Yawancin mutanen yankinka sun fito ne daga iyalan da ba a tanadar musu da wata dukiya wanda ake jira su yi amfani da ita ba lokacin da ƙarfinsu ya kawo, a'a, ana jiran su ne ma idan sun yi ƙarfi su nemo hanyar da za su fitar da gajiyayyu a dangin su daga ramin talauci, su ɗauki nauyinsu da na yaransu, idan sun gaza; a aibata su.


Idan an ga alama sun sami wata dama komai ƙanƙantarta, kuma ba su ɗauki wancan nauyin ba, nan ma zaginsu ya zama aikin lada. 


Dangi suna tilastawa mutum ya ɗauki nauyin da ba nasa ba koda kuwa za'a taru a faɗi ƙasa wanwar.


A lokacin da ka fito neman arziki, al'umma ita ma ba za ta ba ka dama cikin sauƙi ba, tun a makaranta da unguwa za'a fara cusa maka tunanin ka zama talaka kawai ka huta, ai talaka ya fi mai kuɗi kwanciyar hankali, talakawa su ne mutanen kirki, da sauran zantuttuka da adabi wanda za su hana ka motsi a lokacin da ya dace.


Idan ka tsallake wannan kuma, ka ce kai lallai sai ka yi abin da zai fitar da kai daga talauci, nan ma ba za ka samu gwamnatin da za ta ba ka hanya mai sauƙin bi ba, ba ka da jari, gwamnati ba ta tanadar maka da shi ba, komai kuwa kyawun ra'ayinka ko fiƙirar ka.


Bankuna ba za su ba ka jari ba yawanci, sai sun haɗa maka da kuɗin ruwa (Interest), wanda kuma addininka ya haramta maka.


TO YAYA ZA KA YI?


1. KA YI FAƊA DA TALAUCI


Kar ka yarda ka zama talaka, kar ka yarda talauci ya birgeka, kar ka yarda da duk wani abu wanda zai hanaka arziki.


2. KA NEMI HANYAR FITA DAGA TALAUCI TABBATACCIYA


Wannan hanya ita ce, ka samu wata matsala wadda al'umma suke fama da ita, kuma suke a shirye su bayar da kuɗi a kanta, ka warware musu ita, su biyaka kuɗi masu kauri. (Entrepreneurship).


Wannan ita ce hanya sahihiya wadda aka gwadata kuma ake gwadawa kuma take fitar da mutane daga layin talauci take kai su layin arziki da wadata.


Amma fa ka sani, wannan hanya ba sauƙi ne da ita ba, sai dai tabbas hanya ce mai ɓullewa.


3. KA GYARA TUNANINKA


Wannan shi ne babban abin da zai taimakawa rayuwarka, ka cire duk wani tarkacen tunani wanda yake hanaka arziki, ko wanda yake hana ka bin hanyar tsira da mutunci, ko wani tunanin da yake nuna maka cewa ba za ka iya fita daga talauci ba.


Wannan kuma ba zai faru ba sai kana neman ilimi kana karatu.


Dole ka yi karatu, dole ka nemi ilimin addini ingantacce da kuma ilimin rayuwar duniya, ka kula, ilimi na ce ba Certificates ba, yawwa.


4. KA GINA KANKA, KAFIN KA GINA GIDA


Idan ka taso a cikin irin wancan yanayi da na ambata da farko, to lallai ba ka da wani abu da zai taimakawa rayuwarka kamar ka yi ilimi.


Gina kai anan yana nufin, ka yi ilimi, ka gina tunani mai inganci na rayuwa, ka ƙulla alaƙa da masu ilimi da masu arziki, da masu tunani irin wannan.


Ba ruwanka da sharholiya, ko fantamawa ko son birge mutane, wannan duk hanyar zama a cikin talauci ce.


5. KA YI TSANTSENI


Tsantseni anan yana nufin, duk abin da ka samu na kuɗi ka tabbata ka kashe shi ne a kan abin da zai inganta rayuwarka, kamar sayen littafin da zai taimakawa tunaninka, biyan kuɗin makaranta, ko zuwa halartar wani horo, ko wani taron kasuwanci ko wani abu makamancin haka.


Sannan kuma, ka yi ajiya (savings) domin amfanin kanka, ba domin ankon biki ba, ko shaddar sa wa a walima ko bidiri, ko kayan sallah ba, a'a, sai dai domin gina kasuwanci, gina jarin fara wata sana'a ko domin neman ilimin ci gaba.


6. KA KARANTA TARIHI


Wannan shawara ce da zan ba wa duk wani mai tasowa, kar ka yarda ka zauna ba ka da tarihin mutanen ƙwarai, wanda za ka koyi abin arzikin da suka yi a rayuwarsu, sannan za ka samu ƙwarewa ta musamman kan yadda za ka ɓullowa al'amuran rayuwa.


Tarihi zai taimaka maka sosai wajen ba ka ƙwarin gwiwa ka tunkari duk abin da ka sanya a gaba, koda kuwa wasu suna maka ganin cewa za ka gaza.


Tarihi zai ba ka fitila mai haske a wurin da mafi yawan mutane suke ganin duhu.


Tarihi zai ba ka taswira a inda mutane da yawa suke ɓacewa.


Tarihi zai ƙwace ka a wurin da mutane da yawa suke halaka.


Wannan shawara ce da zan ba wa duk wani masoyina da Allah Ya raya shi har ya ga wannan sabuwar shekarar ta 2025.


Kar ku manta, kullum da safe ana yin addu'ar neman tsari da talauci, sannan kuma a yi aikin korar talauci.


Da yammaci ana addu'ar neman tsari da talauci, sannan a yi shirin yadda za'a a yaƙe shi da safe.


A dage, kar a yi sanya, Allah Ya ba mu nasara akan talauci, amin.


Muna addu'ar Allah ya haɗa mu da duk wani alheri da wannan shekarar take tare da shi, Ya kare mu daga duk wani sharri a cikin wannan shekarar da ma wasu shekarun masu zuwa, Amin.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user