Tuesday, 7 January 2025

Amfanin Zama Da Abokai Masu Mabambantan Dabi'u

Tura Wannan Zuwa Ga

Kada ka yarda a abokan ka babu mai kuɗi. Kada ka yarda a abokan ka babu mai karatu. Kada ka yarda ba ka da aboki Ɗan duniya.


Amfanin Zama Da Abokai Masu Mabambantan dabi'u
Hoto: Medium

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


MAI KUƊI


Idan ya kasance duk abokan ka babu mai kuɗi, zai zama babu zaburarwa wato ƙwarin gwiwa.


Idan babu zaburarwa, zai zama babu zaƙuwa wato sha'awa ko buri ko muradi.


Shikenan sai ku yi zaman ku a waje ɗaya cikin talauci, har lokaci ya ƙure muku.


MAI KARATU


Idan a abokan ka babu mai karatu, to ba za ka san yadda duniya ke canjawa ba, da kuma irin damar da zamani yake zuwa da ita ba.


Sai ku yi zaman ku cikin duhun kai. 


Komai ya faru ku ce ƙaddara ce, tun da bakwa nazari.


Idan kuka ji labarin abin da ya shallake hankalin ku, ku ce ƙarya ne hakan ba zai yiwu ba.


Har zamani ya tafi ya bar ku.


ƊAN DUNIYA


Idan duk abokan ka kamammu (Reasonable) ne, kullum sai kuke ɗauka duka duniya gyararriya ce, ba mutumin banza.


Don haka za ku yi ta faɗawa tarkon mugayen mutane kuna cutuwa.


Amma idan kana da aboki Ɗan duniya, ya san komai da ɗabi'ar mutane daban-daban.


Ko wayo ya ga za a yi maka, zai gaya maka abokina ka buɗe idanun ka, kada a yi ma kure-mure.


Idan ma ta kama a yi wani rashin mutumci da ba za ka iya yi ba, sai ya tsaya maka a yi duk wadda za a yi.


Tarihi ya tabbatar da a kowacce al'umma da ta yi nasara, sai da aka samu kalolin mutanen nan guda 3 a cikin ta.


Kuma kowa ya ba da irin gudummawar da shi kaɗai zai iya bayarwa.


A ci-gaba da nazarin rayuwa, Allah ya sa mu dace, kuma idan mun dace mu dafe.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user