Friday, 31 January 2025

Arzikin Da Ba A Rasawa A Rayuwa

Tura Wannan Zuwa Ga

Tabbas waɗannan su ne arzikin da idan ka mallake su ba za ka taɓa rasa su ba, kuma su ne mafarin kusan dukkan wani arziki, da yau za ka rasa komai da ka mallaka amma kana da waɗannan abubuwan biyar da dawo da abin da ka rasa shi ne abu mafi sauƙin yi a wajen ka.


Arzikin Da Ba A Rasawa A Rayuwa
Hoto: Bank at first

Marubuci:- Abubakar S. Wali


Ga su kamar haka:


1. Basira


Damar amfani da ƙwaƙwalwar da Ubangiji ya ba ka wajen gina tunani, ƙirƙira, auna al'amura, magance matsala, da sauransu.


2. Bege


Matuƙar son abin da kake son mallaka.


3. Baiwa


Wani abu da Ubangiji ya hore maka na musamman wanda kake yi cikin sauƙi ko cikin iyawa.


4. Amfani


Amfanar al'ummar da kake rayuwa a cikinta wajen hidimta mata ta hanyar sana'ar ka ko aikinka, ko yin amfani da baiwar da Ubangiji ya ba ka wajen aiwatar da abin da zai amfani al'umma.


5. Jinƙai


Soyayyar ka da tausayinka ga al'ummar da kake rayuwa a cikinta, tare da son ci gaban ta.


Abin lura shi ne koda ba mu da abubuwan da mutane suka auna a matsayin arziki Ubangiji ya ba mu ikon mallakar arzikin da kuɗi ko aiki tuƙuru ba ya ba da shi.


Kuma babu shakka su ne mabuɗin samun arzikin da mutane suke kira arziki.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user