Ka ga yarinyar nan da kake soyayya da ita yanzu, tana da damar samun ingantacciyar rayuwa fiye da kai.
Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint
Wannan shi ne dalilin da ya sa bai kamata ka ƙarar da duk ƙuruciyar ka ba don gina dangantaka kawai da mace ba.
Maganar gaskiya za ta iya rabuwa da kai cikin sauƙi ta samu wanda ya fi ka ko wanda ya riga ya shiryawa yin aure wanda mata suke yi wa laƙabi da "Ready Made" Mutumin da ya riga ya gama ɗora rayuwarsa akan turba, mai kuɗi da isassun kayan aiki.
Lokacin da za ta ware ta bar ka cikin mummunan talauci da tarin tunani kala-kala kamar kanka ya yi bindiga, lokacin za ka gane asarar da ka yi wajen gina soyayya maimakon gina kasuwanci ko koyon wata sana'ar hannun.
Don haka ba kyautuwa ba ne ɓata lokacinka, tunaninka, kuɗinka, akan macen da ka san ba ka da tabbacin aurenta kuma ba ka da damar aurenta.
Ita mace ba ta da asara kamar namiji a irin soyayyar nan don kuwa ita lokaci ne kawai take ɓatawa shi kuwa namiji yana rasa abubuwa da yawa, kamar kuɗi, rashin maida hankali wajen neman kuɗin kansa.
Ka san da cewa mata suna maleji ne da maza idan ba su samu wanda ya fi wanda suke tare da shi ba, da zarar ta samu wanda ya fi ka za ta iya barin ka da karyayyiyar zuciya, da rashin manufa a rayuwarka.
Lokacin za ka gane kuskuren da ka yi na ba wa soyayya dukkan ƙarfinka da tunaninka da lokacinka, don kuwa ita ta samu wani wanda ya fi ka hali da rufin asiri tuni zai tsame rayuwarta daga ƙuncin da kuke ciki ya aure ta kai kuwa fa? Idan ba kai da kanka ba ba ka da wani mataimaki sai Lillahi.
Wannan shi ne dalilin da ya sa a matsayinka na matashi, ba lallai ba ne ka yi amfani da duk lokacinka wajen maida hankali da bin mata da neman soyayyarsu ba, kana ta bin su kamar karen da ya ga sabon ɓarawo. Mata su kansu suna ƙaunar namiji ne wanda ke da manufar da ya sa a gaba ba mai iya tsara kalaman soyayya ba kawai da yawan kiraye-kirayen waya ba.
Ka himmatu da gina kanka, ka ɗauki rayuwarka da muhimmanci, karanta littattafai, koyon sababbin abubuwa, yadda za ka haɓaka sana'arka, sa ka hannun jari da sauran su.
A ƙarshen wannan shi ne kawai abin da ba zai taɓa barin ka ba, a lokacin farin ciki da na baƙin ciki.