1. Rashin lissafi da ƙididdiga
Rashin tsari da fasalin abin da kake samu, da yadda za ka sarrafa shi bisa la'akari da buƙatu na wajibi da wanda ba wajibi ba, zai ci-gaba da jefa ka cikin rashin kuɗi da matsi, ko nawa kake samu.
Marubuci:- Bello Ado Hussaini
Dole ne kake bibiyar abin da ya shigo aljihunka, da abin da zai fita, da kuma abin da kake saran samu tare da lokacin da wannan samun shi ma zai shigo aljihunka.
NB: Ka yi nazari akan Cashflow Analysis.
2. Yawan cin bashi
Yawan karɓar bashi hanya ce mai sauƙi ta ci-gaba da zama cikin rashin kuɗi da talauci.
Duk lokacin da ka karɓi bashi na kuɗi ko kaya, hakan na nufin ka cinye kuɗaɗen da za ka samu nan gaba, ta yadda ko ka samu kuɗi, biyan bashi za ka yi da su, ga shi kuma buƙatu ba sa ƙarewa matuƙar kana da rai.
Dole ka koyi rayuwa a cikin ɗan samun ka, ka gujewa cin bashi sai ya zama dole.
3. Rashin danne zuciya akan buƙatu
Idan ka kasance duk abin da ka ga kana so sai ka saya matuƙar da kuɗi a jikinka, za ka jima a matsalar kuɗi.
Dole ka koyi danne zuciyar ka, kan wasu buƙatu da ba dole ba, koda kuwa kana da kuɗi.
Financial discipline yana matsayin jigo wajen kaucewa matsalar rashin ƙudi da yaƙar talauci.
4. Rashin tattali da tanadi
Na jima ina magana akan tsimi wato Savings. Rashin tattali ba ƙaramar matsala ba ce wajen yaƙar talauci.
Dole ya zama ka yi wani tanadi na abin da yake zuwa ba tare da zato ko shiri ba, kamar rashin lafiya ko hatsari da sauransu.
5. Rashin neman shawarar ƙwararru
Neman shawara da taimakon ƙwararru akan harkar kuɗi ba wai sai ka zama Ɗangote ba.
Duk wanda yake sana'a ko aiki akwai lokutan da yake buƙatar shawarar ƙwararru.
Idan samun ka ya ƙaru, kana buƙatar shawarar abin da za ka yi da wannan ƙarin da ka samu.
Idan samun ka ya ragu, shi ma kana buƙatar shawarar yadda za ka saisaita al'amura, domin kaucewa faɗawa matsala.
6. Maƙalewa sana'ar da ta ƙi gaba ta ƙi baya
Akwai sana'o'i da suke da wa'adi, akwai ayyukan da su ma ana wuce lokacin yin su.
Misali akwai sana'ar da za ta iya riƙe matashi, amma ba za ta ɗauki nauyin iyali ba.
Haka ma aiki akwai na matashi da na mai ɗaukar nauyi.
Akwai kuma ayyuka ko sana'ar da ba ta dace da kai ba.
Duka wannan na nufin idan ka jarraba abu, kuma ka ɗauki lokaci babu haske, kana buƙatar sauya salo, ko kuma wata sana'a ko aiki daban.
Sai dai wasu sukan maƙale akan abubuwan da suka tabbata cewa ba su da nasara ko nasibi a kansu.
Allah ya ba mu ikon kaucewa waɗannan matsaloli, ya inganta samun mu Amin.