Komai ka gani a duniyar nan to da farashin sa, kodai ka biya nan take, ko kuma a biyo ka bashi, amma dai dole sai ka biya.
Farashin Komai A Duniya
Hoto: Dreams time
Marubuci:- Abdulfatah Yakubu
Kamar haka rayuwar matashi take, wani kuskuren idan ka yi shi, nan take za ka girbi abun da ka shuka, wani kuma zai bibiye ka ne, wata ƙila ma sai girma ya kama ka, sannan ne za ka girbi kayan ka.
Duniya ba ta ɗaga ƙafa. Ka shuka abun da ba za ka yi nadamar girbar sa ba.