Masoyina, kai ne wanda ka dace da sarautar zuciyata don haka na ba ka ita kyauta.
Gajerun Kalaman Soyayya Masu Sanyaya Zuciyar Masoya
Hoto: Jordygraph deposit photos
Marubuci:- Abba
Fuskar ki a kullum haske take ƙara yi musamman idan kina murmushi. Idan ki ka yi fushi sannan ne kike daɗa ƙara kyan gani.
Zan iya aiwatar da komai har idan ina jin kalaman ka masu sanyaya zuciya.
Masoyiyata a duk lokacin da na ji muryar ki na kan samu natsuwa a zuciyata.
Na yarda da kai na aminta da kai don haka na mallaka maka kaina.
Murmushin ki gare ni ya fi a ba ni kyautar sabuwar mota da gida.
A kullum ba ni da burin sauraren wani zance idan ba naka ba.