Kowanne irin matsatsi zan shiga a rayuwata, ko yaya jama'a za su tsane ni ba zan daina son ki ba.
Marubuci:- El-Nass
A lokacin dana fara ganin ki, ji na yi wani abu yana shiga zuciyata, ya wuce can ciki, inda babu wadda ta taɓa zuwa kuma har abada babu wadda za ta sake zuwa.
Kamar yadda taurari ke yin haske gami da ƙyalli a sararin samaniya, to haka fuskarki take haske gami da ƙyalli a cikin zuciyata.
A dukkannin lokacin da zuciyata ta shiga cikin yanayin ƙunci, to ba abin da kan fitar da ita daga wannan yanayi face daɗaɗan kalaman ki masu sanyaya ruhi wanda ya fi busar sarewa daɗin sauraro.
Zan so a kodayaushe kuma a kowanne lokaci na kalle ki, domin kallon kyakkyawar fuskarki na haifar mini da kwanciyar hankali a cikin raina.