Na san ba na iya ba ki duniya, amma kuma zan iya ba ki rayuwa da zuciyata. Ina son ki fiye da yadda nake buƙatar ruwa lokacin buɗa baki.
Marubuci:- It'z Nazeephancy DH
Tausayi gare ki masoyiyata, kin zama madubin kallon idaniyata da zuciyata, tunaninki a ƙwaƙwalwata, ina son ki da duka soyayyar zuciyata.
Tafiya da masoyin gaskiya ita ce tafiyar da ke saurin kawo farin ciki a zuciya. Ina sonki, ina ƙaunar ki masoyiyata haƙiƙa ke ce halittar da ke saurin kawo farin ciki a zuciyata.
Zancen farko cikin izinin sarkin farkon da ba ya da na biyu ma'ana sarkin da ya halicci kyau sannan ya sanya shi ga kyakkyawar halilta mai hankali da natsuwa kamar ki.
Saƙon zuciya daga zuciya zuwa zuciya mai tausayi, zuciyar da ta yarda samu da rashi duk na Ubangin bayi ne, ke nake so kuma nake ƙauna a kowacce rana. Ke ce masoyiyata mai share mini kuka.
Aminci a gare ki yake kyakkyawa mai kyawun fasali, zuciyarki da jikinki duk mai kyau ne, ina son ki fiye da son da nake ma lafiyar jikina. Barka da sabuwar shekara.
Rai da zuciyata duk mallakinki ne gimbiyata, ke ce abar so na kuma ke ce abar yabona dare da rana, da soyayyar ki nake yin numfashi ina ƙaunar ki fiye da rayuwata.
Mene so idan babu ke Gimbiyata? Ina son ki domin ke ce rayuwata kuma ke ce farin cikina sai da ke nake iya fahimtar komai a duniya. Ke na fi ƙauna.