A wata lacca da ta gabata, na yi ishara kaɗan akan yadda mutane lokaci ya zame musu ba abu ɗaya ba, ta yadda tasirin sa gare su yake bambanta, sunan laccar: Nazari akan lokaci. Fahimtar hakan wani sabon mabuɗi game da rayuwa ne.
Marubuci:- Bukhari Alhawari
A duk lokacin da wata shekara ta wuce, zukata da yawa kan cika da yin wa'adin wasu ayyuka na ci-gaba, musamman matasa, waɗanda ba su yi ba a tsohuwar shekara, sai dai kamar haka wata sabuwar shekarar za ta zo ba tare da sun cimma komai ba, haka dai har tsufa, ko mutuwa ko rashin lafiya.
Yanayin ya yi kama da wanda ya maƙale a waje ɗaya, ba ya iya yin gaba, idan har zai motsa sai dai ya yi baya wato dai suna samun ƙaruwar shekara ne ba sabuwar shekara ba.
A cikin wannan rubutu ga wasu gaskiya goma nan, ga duk wanda ke fama da irin wannan matsalar, in sha Allah zai samu mafita, ku biyo ni.
1. Ƙididdiga
Yi wa kai ƙididdiga tsakanin nasarori da ka samu ko akasin haka a shekarar da ta wuce. Sabuwar shekara ko ƙaruwar shekara? Lallai kowace shekara a rayuwar mu Allah kan ba mu wata dama daban da wadda ta wuce, haka wadda za ta zo, a lokacin da ka iya nutsuwa ka ɗauki takarda da biro, ka iya ware aya da tsakuwa, to wannan daidai yake da gano bakin zare, a lokacin za ka gane a ina kake yanzu.
2. Fayyacewa
Lallai duk abun da ka ke so ka cimma ka iya fayyace shi sarai a ran ka, ka keɓance shi da addu'ar ka, ka iya ware shi wajen bin sababin sa. Inda za ka shiga kasuwa ba tare da fayyace me ka je yi ba, wannan zuwan naka, ba shi da bambanci da wanda ya yi tafiya bai san ina zai je ba. A ido kowa zai ga aiki yake, amma a haƙiƙa aika-aika yake wa kansa. Misali za ka iya fayyacewa a matsayin ka na Ɗan Kasuwa, shekarar 2025, ƙudurin ka shi ne: buɗe shagon ka na biyu, wannan misali ne kawai.
3. Bi a sannu
Sunnar Ɗan Adam ce gaggawa, sunnnar Allah ce bi a sannu, a duk lokacin da ka sa wani abu mai muhimmanci a rayuwar ka, kada ka yi gaggawar ganin nasarar sa, hakan na haifar da sarewa da wuri idan ba a gani ba, kullum ka tambayi kanka da safiya, da gaske ne ina kan hanyar zuwa cimma nasara? Shin ban bijiro da wani dalili da zai hana ni kai wa ba, idan har ka samu amsa cewa kana kan hanya, to tsayawa a (Go slow) ba matsalar ka ba ne, matsalar hanyar ce..
4- Rungumi koyo
Lallai wanda yake ji ya gama iyawa, to wannan ya rasu Allah ya masa rahama. A iya nazari na da tunani na ɗalibi, ban san abun da ke katange mutum daga ilimin nasara ba, sama da jin ya iya, wannan tsarin yana shirya mutum tsaf zuwa ga faɗuwa. Ya na kulle hasken tunani, ya dadishe kaifin basira, yana sa raina ilimi da malamai, yana sa girman kai, a ƙarshe kuma asara.
5. Fasahar kawarwa
Akwai wasu halaye guda biyu, da suke daskarar da mutum ga barin nasara, akwai mummunar ɗabi'a, akwai mummunan tasarrufi da lokaci. Rashin sanin ina lokacin ka ke tafiya, daidai yake da rashin sanin ina rayuwar ka za ta je. Rashin kyakkyawan hali, daidai yake da rashin kyakkyawan muhalli.
6. Bunƙasa kai da kai
A lallai duk lokacin da kake son cimma wani abu, kada ka yaudari kanka, tambayi kawai mene ne ƙa'idodin da ake bi wajen samun sa, kawai sai ka fara aiki a kanka don ka ga ka cika waɗannan gaɓɓai, da yardar Allah har gida dama za ta biyo ka.
Ka nemi ƙwarewa, nasara za ta biyo ka, idan ka bi nasara za ka rasa ƙwarewar da za ka same ta. Bunƙasa kai da kai na shiga cikin sayen littattafai, shiga wasu kwasa-kwasai, haɗuwa da wasu mutane, tarewa a wata unguwa, barin wani gari, ko barin wasu mutane, muhallai, aƙidu, ko wasu tunane-tunane da sauran su.
7. Lafiyar ka jari
Galibin cututtukan tsufa an same su ne a lokacin matasantaka, lokacin da garkuwar jikin ka take da ƙarfin yaƙar su, a lokacin da ta yi rauni saboda tsufa, sai cututtukan su bayyana shikenan. Me wanna yake nufi, a yanzu haka da nake wannan magana, kana da wata ɗabi'a wadda nan da shekara goma ko sama da haka, ka zama mara lafiya, za ta iya kasancewa shan kayan zaƙi da sukari, ko kuma kallon waya da dare ba tare da glass na kariya ba, ko kuma cin duk abun da ka gani a hanya ba tare da izini da inganci ba. Waɗannan matsalolin naka, za su iya hana ka kai wa ga nasara, ko kuma su hana ka morar nasarar bayan ka cimma ta, sai dai ya zama kullum ka na wajen likita.
8. Fasahar kula da ƙananun abubuwa
Shin za ka yarda da idan na ce maka, wanke baki da dare, lokacin da za a kwanta ya na da alaƙa da lafiyar tunanin ka gobe, ko kuma cewa karkaɗe shimfiɗar ka yayin kwanciya yana da alaƙa da ingancin wunin gobe? To duka waɗannan bayanai haka suke.
A lokacin da ka fara ba da muhimmanci ga ƙananun al'amura a rayuwar ka, manyan za su buɗe maka, ta haka ne kuma kaɗai za ka san: yin nasara akan manyan matakai, na da alaƙa da yin nasara akan ƙananu.
9- Gamayya
A duk shekara ta Allah akwai irin mutanen da ya kamata a ce ka kai gare su, sun san ka, za ka iya kiran waya su faɗi sunan ka, a harshen yan zamani wato: "Connections" na sani za ka yi mamaki amma haka abun yake.
Akwai abubuwan da za ka rasa a rayuwa koda ka cancanta ka samu a haƙiƙa, amma rashin haɗuwa da wanda zai iya ba ka, sai abun ya zama aiki. Na san kun san abun da ake kira a musulunci da Shafa'a da kuma Tawassuli. Wannan misali ne.
10. Ka yi farin ciki
Lallai akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin addu'a da bin sababi, su kuma biyun akwai alaƙa mai ƙarfafi tsakanin su da ƙaddara, ita kuma akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin ta da hukuncin Ubangiji, shi kuma akwai alaƙa mai ƙarfafi tsakani da hikimar sa, shi kuma akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin sa da adalcin sa. Shi kuma akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin sa da rahamar sa.
Lallai rahamar Allah ta yalwace komai da ya halitta ciki har da kai aboki na. Lallai Allah mai alkhairi ne, abun da ka ke nema nasa ne, ba zai rage shi da komai ba, idan ya ba ka. Shikenan. Tashi ka zabura nasarar Allah ta na tare da kai. Kai ku ce Allahu Akbar .