Friday, 10 January 2025

Kalaman Karfafa Gwiwa Na Sabuwar Shekara

Tura Wannan Zuwa Ga

Wuta ita take raba dusar ƙarfe da ƙasa, ta tsarkake shi tare da ƙara masa karfi da daraja. Wuta ita take narka zinare ta raba shi da dukkan datti, har ya zamo mai daraja kuma abun kwalliyya.


Kalaman ƙarfafa gwiwa na sabuwar shekara
Hoto: Rawpixel/Getty Images

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


Haka kuma ƙalubalen rayuwa yana inganta ruhin Ɗan Adam, ya saita tunanin sa, ta yadda mutum zai ƙara fahimtar hikimar rayuwa da ma'anarta.


Ma'aiki sallallahu alayhi wasallam cikin Hadithi yake cewa;


"Idan Allah (S.W.T) ya so bawa, sai ya jarrabce shi, idan ya jure kuma ya jajurce, sai ya sami mafita da rabo. Abun da ya biyo baya na ƙaiƙayin zuciya kuma, idan aka yi haƙuri, kankarar zunubi ce ga mumini."


Manufa anan shi ne kada mu karaya a kowanne hali, mu kasance masu fata nagari, tare da kyautata zaton samun sauƙi daga kowanne tsanani, domin bayan dukkan tsanani sauƙi ne yake biyo baya.


Marigayi BASHIR OTHMAN TOFA, cikin talifin sa "TUNANIN KA KAMANNIN KA,, Ya ce "Wahala ita ke matso ƙwazo, shagwaɓa kuma kashe shi take yi."


Jarumi DENZEL WASHINGTON, yana cewa; sauƙi ya fi zama barazana ga ci-gaba sama da tsanani.


"Ease is more threat to progress than hardship".


Ba ma fatan tsanani ga kawunan mu, ko ga 'yan uwan mu, sai dai gaskiyar magana shi ne, ba za mu iya kaucewa ƙalubale ba matuƙar muna raye, sai dai mu yi tanadi, kuma mu yi komai cikin hankali da nazari.


Sannan mu yi haƙuri da rayuwa a kowanne hali da lokaci.


Mu sani tsanani ba ya dawwama, kamar yadda sauƙi da jin daɗi su ma ba su da tabbas.


Mu yi ƙoƙarin samarwa kanmu da kanmu farin ciki yayin yalwa ko rashi, mu ƙaunaci juna, mu yi afuwa da uzuri ga juna.


Tabbas ƙauna da soyayya wani sinadari ne da yake maganin cututtukan zuciya da yawa, ya ba ta salama, ya kuma amintar da makusantan mai ita.


Fatana gare mu duka shi ne mun shiga sabuwar shekara da sabon tunani, da sha'awar koyo da saurare tare da fahimta kafin yanke hukunci akan komai da kuma kowa.


Mu sani kowa da yadda yake kallon rayuwa, kuma tunanin kowa zai iya kasancewa mai amfani a wani lokaci.


Mafi muhimmanci shi ne mu gane lokacin da ake buƙatar komai da sa'adda ake buƙatar kishiyarsa.


Mu mutunta juna da ra'ayin juna.


Mu sani Allah (S.W.T) yana ganin mu a cikin kowanne al'amari, kuma shi ne Mai hukunci, daidai da dacewa a wajensa take.


Allah ya kawo mana ɗauki ya tsayar da zuciyar mu akan imani, ya sa mu kasance masu amfani ga kawunan mu da al'ummar mu.


Kada mu cutar kada a cuce mu.


Allah ya sa mun shiga sabuwar shekara cikin ƙaunar juna da taimakon juna da afuwa ga juna, tare da kare harshen mu daga miyagun kalamai na sukar juna Amin.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user