Wednesday, 8 January 2025

Kalaman Kiran Waya Na Barka Da Dare

Tura Wannan Zuwa Ga

Ke ce sarauniyata, na mallaka miki dukkan wani muƙamin da ke ƙarƙashin ikon zuciyata, ke kaɗai ce tawan, daga kanki babu canji. Ina yin ki.


Kalaman Kiran Waya Na Barka Da Dare
Hoto: Deposit photos

Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR


Ke ce mahaɗar ruhi da kuma gangar jikina, akan son ki zan iya ba da dukkan rayuwata. Ina son ki.


Ke ce ruwan jikina, da taimakon sinadarin murmushin ki nake iya motsa dukkan halittar kuzarin jikina. Ina ƙaunar ki.


Ke ce ƙarfin juriyar jikina a kan son ki zan iya jure dukkan wani farmaki daga ko'ina yake. Ina tunanin ki.


Ke ce wutar lantarkin da ke rarrabuwa tana taimakon dukkan wasu jijiyoyin da ke aiki a jikina. Ina kishin ki.


Ke ce ruwan sanyin da ke narkar da dukkan wasu tafasassun ruwan zafin da ke ƙona zuciyata. Ina tare da ke.


Ke ce nasabar cancantuwar zama a cikin ruhina, da tunaninki nake kwana kuma nake tashi a cikin zuciya. Ina muradin ki.


Ke ce babbar alƙaryar birnin da yake ƙawata sansanin nahiyar zuciyata, da son ki nake alfahari a cikin raina. Ina son ganin ki.


Ke ce jinin jikina, da kulawar tunaninki ƙwaƙwalwata take iya kai saƙonnin farin cikin da ke sauka a cikin zuciyata. Ina begen ki.


Ke ce ma'ajin sirrikan da ke ƙunshe a cikin zuciyata, ba na shakkar sanar da ke sirrina domin da ke da zuciyata kuna tafiya ne a kan abu guda. Ina kewar ki.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user