Friday, 3 January 2025

Kalaman Kiran Waya Na Barka Da Rana

Tura Wannan Zuwa Ga

Ke ce hasken raina, ke ce jina, ganina da duk wani abu nawa, son ki daga Allah ne, a lokaci ɗaya da ganin tsararren hotonki na ji kibiyar son ki ta ratsa ruhina. Ke kaɗai ce a gare ni da zuciyata, son ki azimun ne. Ina son ki da gaske.


Kalaman Kiran Waya Na Barka Da Rana
Hoto: Every pixel

MarubuciImran Musa Jahun


Amincin Allah Ya tabbata a gare ki jinin jikina. Da soyayyarki ilahirin jiki na yake motsi, sanyi ko zafi hakan ba ya sanya ni kasalar kallon hotonki, tsanani ko azaba ba sa sanyawa na rufe bakina da ambaton kyakkyawan sunanki. 


Tabbatuwa mafi bayyanuwa a raina shi ne soyayyarki. Ƙaƙƙarfar iskar son ki ta lula da ni cikin sararin samaniya ta yadda ba na hangen duk wata 'ya mace face ke, babu wata juriya ko ƙarfi da ke wanzuwa gare ni face da ƙarfin ambaton harafofin sunayenki.


Idanuwana sukan makance na rasa ji da gani a duk sa'adda kyakkyawar surar jikin ki ta sauka a idanuwana, sautin muryarki ya kan narkar mini da zuciya har na ji kunnuwana sun gaza tantance zaƙin muryarki illa iyaka ta fi duk wani sauti zaƙi da daɗi. 


Bakina ya kan zama tamkar idanuwana a buɗe a duk sa'inda yalwataccen murmushin ki ya bayyana a gare ni.


Ƙafafuwa da hannayena ba sa iya ɗaukar jikina a duk lokacin da kika furta min lafiyayyun kalamanki. Ki so ni mai kyau!

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user