Idan ina zaune babu abin da yake saurin kawo mini ziyara irin tunaninki. Na ji masoya na kuka a kan soyayya wahala ce, ni kuma tun lokacin da na yi arba da ke na ji na shiga cikin jerin sarakunan da ke alfahari da kansu a fagen soyayya.
Tunaninki yana zuwa ne daga can cikin tsakiyar zuciyata shi ya sa nake furta haruffan kalmomin sunanki a farkon zancen haruffan da ke zuwa a farkon sautin muryar da ke neman ɗaukin gaggawa daga zuciyar da ta fi kowacce zuciya tausayi da tausayawa.
Ki sani so wani abu ne na musamman wanda misalta shi zai zamo aiki na musamman, tasirinsa yana tafiya ne a lokacin da ka samu daidai ko kuma akasin daidai.
Haƙiƙa son ki yana ƙara fahimtar da ni ilimin sanin mene ne haƙiƙanin so? Sai dai har yanzu akwai wasu darussa na musamman waɗanda zuciyata take fahimtarsu daga zuciyarki.
Ba zan gajiya ba wajen lissafin ranakun zuwan soyayyata a gare ki ba, ni dai fatana kawai ki ba ni gurin kwana.
Lambunan sanyi masu cike da kayan alatu na musamman waɗanda suke ɗauke da ƙawatattun furanni koraye, kowannensu yana ɗauke da tambarin haruffan zanen sunanki.
Fara'ar farin ciki mai ɓuɓɓugowa cikin sautin ajiyar lafuzza masu sanyi waɗanda suke fitowa daga zuciyarki.
Ban san mene ne daɗin soyayya ba? Sai lokacin da na yi arba da ke.
Ban san daɗin rayuwa ba sai da na haɗu da ke.
Ina kallon kaina mai sa'a tun lokacin da na yi sa'ar samun wadda ta fi kowace 'ya mace sa'a a rayuwa.