Haƙiƙa kin iya kallon soyayya domin kyakkyawan kallon ƙaunar da kike turo saƙonsa zuwa gare ni shi ne silar tabbatuwar cewa a fagen iya soyayya ba kowa ba ce kamar ki gwanata.
Marubuci:- Yaron MLM KD
Hmm na kan yi murmushi yayinda idanuwana su kai tozali da abin da kowacce idaniya ke buƙatar gani wato kyakkyawar halitta irin taki.
Yayin da zuciyata ta taho zuwa ga kyakkyawar sarauniyar zinariya, kuma me kyakkyawan takun ƙasaita fiye da na ƙananun sarakai.
Haƙiƙa tarayyata da ke ita ce kyakkyawar rayuwar da nake mafarki a kodayaushe masoyiya.
Duk da na kasance ba kowa ba amma na kan ji ƙwarin gwiwa ta ya ƙaru a duk lokacin da na gan ki a gefena.