Sunday, 19 January 2025

Kyawawan Kalaman Soyayya A Daren Farko Ga Ma'aurata Na Zamani

Tura Wannan Zuwa Ga

Ke kyakkyawa ce a cikin kyawawan 'yammatan zamanin nan, ke ce matakin farko, dukkan 'yammata kin zamo madubi a gare su.


Kyawawan Kalaman Soyayya A Daren Farko Ga Ma'aurata Na Zamani
Hoto: 18989612/Freepik

Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR


Assalamu Alaiki saƙon sallamar so mabuɗin murfin ƙofar zuciyata zuwa gare ki, maƙurar soyayyar da zuciyata take ɓuɓɓugo da shauƙin begenki a fili, son ki ne sila kuma ma'aunin da ke auna mizanin rayuwar dukkan wani nishaɗin da ke ɓuɓɓugowa da shauƙin murmushin fuskata.


A karon farko cikin tarihin tsawon kwanakin rayuwar da na yi na samu kyauta ta musamman wadda Allah Ya zaɓe ta cikin kyawawan bayin shi Ya ba ni domin ta zamo abokiyar rayuwata ta har abada.


Ke ce nake nufi da kalamaina 'yar wajen Mama murmushinki nake buƙata domin ya zamto mabuɗin da zai buɗe mini ƙofar shigowa cikin nutsuwar samun zama a tare da ke.


Kafin na fara shiga cikin zangon rubuta miki saƙon da ke fitowa ta cikin numfashin zuciyata sallama a gare ki zan fara 'yar mutanen Larabawa.


Gwargwadon ruwan ƙoramu masu kwaranya cikin yanayin saukar ruwan sama suna ƙara bayyano da kwarjinin halittar kyawunki.


Babban burin ruhi da cikar ƙasaitar murmushin zuciyata shi ne ganin ki a kusa da ni kina mai fesa mini kyakkyawan murmushin ki.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user