Ɗago fuskarki kaɗan na kalle ki, tsananin shauƙi da annashuwa suna fitowa daga tsakiyar kyawawan haƙoranki, babu inda suke yada zango sai a cikin zuciyata.
Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR
Na yi shiru na shiga cikin wata duniya ta musamman ba komai nake yi ba sai tsananin tunaninki.
Murmushi da shauƙi yana mamaye zuciyata a daidai lokacin da nake tunawa ke nake so.
Kamannin jikina suna bayyanar da nuna yabawa da ƙwarewarki wajen iya kwantar da dukkan wata damuwata.
Aminci a gare ki tare da gaisuwa mai fitowa cikin inuwar zuciyar da ke miki soyayyar gaskiya zuwa gare ki. Barka da sabuwar shekara.
Ke ce alƙadarin alƙaryar da ke ƙawata farin cikin da ya kewaye ruhina.
Na hangi wani sinadari daga cikin tsakiyar idanuwanki wanda har yanzu yake yawan zo mini har cikin baccina.
Allah Ya halicci halittarki cikin ƙawatacciyar ni'imar halittar da idona bai gano wata tamkar ki ba.
Kullum ƙara haske kike yi, ni kuma zuciyata ƙara sonki take yi, ba na buƙatar wurin hutu wanda zai sa na rage tunaninki.
Na ɗauki son ki na ɓoye shi a cikin zuciyata, ba na buƙatar wani abu ya zo kusa da shi domin ina fama da tsananin kishinki a cikin raina. Barka da sabuwar shekara.