Akwai wani kuskure da muke yi, Matashi yana fara samun kuɗi, ko wata dama, maimakon ya yi amfani da wannan damar wajan ƙara gina sana'a ko kasuwancin da yake yi, a'a, sai ya fara tarawa kansa maƙiya na babu gaira babu dalili, shi ne kullum habaici a status; "sun ƙi, Allah ya so.", "Lokacin mu ne, yen yen yen yen....", Kwarai! Lokacin ka ne, amma na faɗuwa, domin da wannan halin babu inda za ka je.
Marubuci:- Abdulfatah Yakubu
Kada nasarar dare ɗaya ta ruɗeka, rayuwa mataki mataki ce. Idan Allah ya yi niyyar buɗe mana ƙofofin alkhairi dubu, ba lokaci ɗaya yake buɗe mana su duka ba, zai buɗe mana ƙofar farko ne, alla bashshi mu kuma sannu a hankali ta hanyar inganta kai, da alaƙar mu da jama'a sai mu buɗe ragowar ƙofofin.
Kowace dama, dama ce ta samun wata damar. Kowane taku, taku ne zuwa ga wani takun. A kasuwa, dubu ɗarin ka ta farko, dama ce ta samun miliyan ɗin farko.
Iya karanta baƙaƙen kowane yare, dama ce ta fara koyon haɗa baƙi.
Iya zama, dama ce ta fara koyon tsayuwa, tsayuwa kuma dama ce ta fara koyon tafiya, haka dai lissafin yake a kowane ɓangare na rayuwa.
Kai da ka fara yanzu, ina kai ina yi wa waɗanda suka daɗe a ciki habaici? Yanzu aka fara, kada nasarar dare ɗaya ta ruɗe ka.