Me ya sa kika zaɓi son ganin kukana maimakon a ce ki so baccina wanda zan yi shi har cikin ƙalbina? Wayyo ni. Kaichona.
Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR
Zancen aure muka ƙulla ni da ke domin zuciyata babu kalar ki. Ashe ke a ran ki akwai abin da yake faruwa.
Zuciyata kike son ki fasa, kin bar ni ina ta bacci kamar wata kasa, ina tunanin abin da ke a ƙasa, na soyayyar da muke wadda ba sa'insa.
Ashe dukkan kalamanki na yaudara ne? Da ma kin so ni domin ki ƙware ni ne? Me ya sa ki haka?
Ɗawainiya nake da ke a kowace rana, ina ta tunanin akwai wata rana wadda za ta zo a ce mun zauna muna murmushi muna yin murna.
Yau dai gare ki na zamo ɗan kallo, kin so ki maida ni kamar wata ƙwallo, maimakon farin wata sha kallo.
Kar ki sa zuciyata ta yi kuka bayan ta ɗauki so ta ba ki duka a kanki.
Son ki ne abun son ruhina, fushinki ne silar kukana. Ke nake so, kuma nake yawan ƙauna.
Yau ga shi ni da ke muna bankwana, na so a ce muna tare ba za mu rabe ba amma ƙaddara ba za ta bari ba.