Monday, 27 January 2025

Sakonnin Bayyanawa Budurwa Matsayin Ta A Zuciya

Tura Wannan Zuwa Ga

Soyayyar ki ta zama babbar abokiyar hira gare ni don a duk yanayin da na kaɗaice soyayyar ki kan kawo mini ziyara ta musamman don taya ni hira.


Sakonnin Bayyanawa Budurwa Matsayin Ta A Zuciya
Hoto: Maya/Share chat

Marubuci:- Ridwan Khan Adam


Amincin Allah su ƙara tattara su tabbata ga bayinsa salihai, yarda da afuwa haɗi da jinƙansa da rangwami su ƙara wanzuwa a tsakanin masoyan da suka riƙe amanar juna  kamar mu.


Kin kasance abu mafi muhimmanci wanda kan kai kawo a tsakanin jijiyoyin da ke damfare a zuciyata don babu yadda za a yi zuciyata ta buga ba tare da kin ratsa ta cikin ta ba don ke ce masarrafar sarrafa jinin jikina.


Ni ƙaunarki kawai ta ishe ni ta katange ni da duk wani harin ƙunar baƙin waƙen da sauran 'yammata kan iya kawo min, don ƙaunarki ta zama jari ga zuciyata.


Son ki ya fi jini da iska gami da ruwa muhimmanci a gare ni don ke ce dawwamammiya a zuciyata, kuma wacce ba zan yi  yinkurin yi mata kishiya ba.


Harshena ko hannuwana sun yi kaɗan wajen bayayyanawa ko furtawa ko ma rattabawa yadda zuciyata ke ji da ke, don ina ji da ke fiye da yadda uwa ke ririta jaririn da ta haifa yau.


Daga ƙarshe fatana mu zama masoya na gaskiya wanda sauran masoyan duniya za su yi koyi da su a nan gaba. 


Daga naki kuma mai son ganin jin daɗin ki a kowane lokaci.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user