Wednesday, 8 January 2025

Tarihin Rayuwar Rumi (R.A) A Takaice

Tura Wannan Zuwa Ga

Suna


Jalāl al-Dīn Muḥammad Rūmī (Da Persian : جلال‌الدین محمّد رومی ), ko kuma kawai Rumi (30 Satumba 1207 - 17 Disamba 1273), mawaƙi ne na ƙarni na 13, Hanafi faqih, Masanin Islama mai girma. (Rumi a rayuwarsa ya rubuta baitoci 65,000).


Tarihin Rayuwar Rumi (R.A) A Taƙaice
Hoto: Poem analysis

MarubuciSaliadeen Sicey


Rumi wanda ke nufin Jagoranmu, ɗaya ne daga cikin manyan mawaƙan Musulunci. Yawanci an san shi a duniyar masu magana da Ingilishi da suna Rumi. Shi masanin sufanci ne, masanin falsafa kuma mai son bil'adama. Mabiyansa sun kafa makarantar sufaye don ƙarfafawa da kuma farin ciki da koyarwarsa.


Haihuwa


An haifi Sufi Jalal al-Din Rumi Jalal al-Din Mohammad-e Balkhi a gefen daular Farisa, a Balkh a Afghanistan ta zamani (kodayake ana da'awar an haife shi a wani wuri a Tajikistan). A ranar 30 ga watan Satumba 1207. Ɗa ne ga Baha' al-Din-e Valad, wani sanannen malami kuma masanin tauhidi da kimiyya, dangin Rumi kusan su 2000 sun gudu lokacin da yake ƙarami, saboda mamayar Mongols, suka zauna a Samarkand sannan kuma suka koma Anatoliya. A 1224 Rumi ya auri Gauhar Khatun, wanda suka haifi 'ya'ya maza biyu tare. 


A cikin 1229, Sarkin Seljuk Turks ya gayyaci mahaifinsa don koyar da ilimin tauhidi a babban birnin ƙasar, Konya.


Rumi ya zama malami; Bayan an aika shi zuwa Aleppo da Dimashƙu, da bagadaza. Rumi ya kammala karatunsa na addini da shaida mai kyau, bayan rasuwar mahaifinsa, Rumi ya karɓi muƙaminsa kuma ya zama ɗaya daga cikin manyan malamai a ƙasar tun yana ɗan shekara 24.


Samun waƙoƙin Rumi gabaɗaya ya samo asali ne daga abokantakarsa da Shams al-Din Tabrizi. Wajen shekara ta 1244, Shams wani sufi mai tafiya ya isa Konya, yana wa'azi. 


Sa'adda ya je da shekaru 37 Rumi sun haɗu da malaminsa kuma amininsa Shams; Haɗuwar tasa sun canja rayuwarsu gaba ɗaya, su biyun ba kasafai suke rabuwa ba. An ce 'ya'yan Rumi da mabiyansa sun ji haushin Shams kuma suka kore shi daga garin. 


Bayan tafiyar Sham, Rumi ya jajanta wa kansa wajen rubuta waƙoƙi, rera waƙoƙi, da raye-raye, musamman ma raye-rayen da aka yi da su a kaɗe-kaɗe da ake yi wa laƙabi da whirling dervish. 


Duk da cewa kowanne ya zama madubi ga ɗan'uwansa, Shams ya ɓace ba sau ɗaya ba sau biyu ba. A karo na farko, ɗan Rumi Sultan Veled ya nemo shi ya same shi a Damascus. Ɓacewar sa ta biyu, ba a sake ganinsa ba har abada, kuma an yi imanin cewa wataƙila malaman tauhidi na addinin Islama ne suka kashe shi, ko kuma wasu mutanen Konya waɗanda suka ji haushinsa akan tasirinsa akan Rumi.


Nan da nan Rumi ya samu suna a matsayin mai hangen nesa mai cike da farin ciki, kuma ya sadaukar da sauran rayuwarsa wajen rubutu da ibada. Manyan ayyukan Rumi sun kasance tun bayan ɓacewar Shams: Diwan-e Shams-e Tabiz , ko “Waƙoƙin Shams da aka Tattara,” an rubuta su a cikin muryar Shams; Mathnawi,” wani lokaci ana kiransa da abin karantawa na Farisawa, kuma waƙar da aka fi karantawa a duniyar Musulmi; da kuma ayyuka daban-daban da suka haɗa da Fihe ma fih, "Magana"; wa'azin da aka tsara a lokuta.


Rumi ya kasance ɗaya daga cikin fitattun mawaka a duniya. Malamai irin su AJ Arberry, Franklin D. Lewis, Jawid Mojaddedi, da Reynold A. Nicholson sun fassara ayyukan Rumi zuwa tarin littafai a cikin Ingilishi.


Tasirin Rumi a zamani 


Rumi ya kasance mai mahimmanci a koyaushe. Waƙar soyayya ta Rumi ta sami tagomashi sosai a ƙasashen yamma da kuma a tsakanin sabbin matasan musulmi a duk faɗin duniyar musulmi, ga Turkawa, Afganistan, Iraniyawa, Tajik, da sauran musulmin Asiya ta tsakiya da kuma musulman Kudancin Asiya. An fassara ayyukansa a cikin harsuna da yawa a ko'ina, sauran al'adu da mutane a duniya a yanzu ma suna ƙara fahimtar Rumi sosai kuma a wasu lokuta, har ma suna ƙoƙarin bin koyarwarsa da hanyarsa.


Mene ne saƙon Rumi?


Saƙonnin soyayya, juriya, ƙarfafa kai, ci gaban ruhi, da faɗakarwa ta Rumi har yanzu suna da amfani ga masu sauraro a yau a cewar Shahram Shiva.


Kafa Ɗarikar Sufi Dervish 


Sufi whirling wani nau'i ne na zikiri wanda ya samo asali daga wasu ƙungiyoyin Sufaye, wanda har yanzu Sufaye Derwishes na Ɗarikar Mevlevi suke yi da sauran masu Bin Rifa'i-Marufi.


A matsayin nau'i na zikiri (ambaton Allah). Dervish kalma ce ta gama gari a tafarkin Sufanci; jujjuyawar wani ɓangare ne na zikiri.


Zawiyyar Mevlevi ko Mawlawiyya (Turkiyya: Mevlevilik ko Mevleviyye; Farisa: طریقت مولویه) ɗarikar Sufaye ce wacce ta samo asali daga Konya (wani birni a yanzu a Turkiyya; tsohon babban birnin masarautar Seljuk) wanda mabiyan Jalaluddin Muhammad Balkhi Rumi suka kafa. Rumi, mawaƙin Farisa na ƙarni na 13, kuma Sufi kuma masanin tauhidin Islama.


Mevlevis kuma ana kiran su da "dervishes whirling" saboda sananniyar al'adar da suke yi na jujjuyawa a yayin yin zikiri (ambaton Allah ). 


An kafa Mevlevi 1273; shekaru 752 da suka gabata Cibiyar Mevlevi ta na birnin Konya na ƙasar Turkey.


A cikin 2008, hukumar Tarihi Da Al'adu Ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) ta tabbatar da "Bikin Mevlevi Sema " a matsayin ɗaya daga cikin manyan abubuwan Ban Sha'awa na Al'adun Ɗan Adam.


Kimanin shekaru 752 da farawa Mevlevi al'ada ce bisa koyarwar Rumi, wanda aka fi sani da Mevlevi ko Mevlana, wanda yana ɗaya daga cikin manyan mawaƙan Musulunci.


Rasuwa


Rumi ya rasu ne a ranar 17 ga Disamba, 1273 Miladiyya yana da shekaru 66, an binne shi kusa da kabarin mahaifinsa a green dome a birnin konya. Yanzu wajen ya zama gidan tarihi na Mevlâna, wurin ya haɗa da masallaci, ɗakin rawa, da wuraren zama na dervish. Ana gudanar da Urs (biki na ruhi) kowace shekara a ranar 8 ga Disamba don tunawa da shi a Konya.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user