Uzuri guda uku da matasa kan ba wa kansu kariya da su, ba tare da sun san hakan ne ke katange su daga nasara ba.
Ga su kamar haka:
1. Ƙaryar busy da rashin lokaci
Matasa da yawa ba sa zuwa makaranta ko zumunci ko wani abu mai amfani ga rayuwarsu sakamakon uzurin su na wai ba su da lokaci, amma idan ka yi wa rayuwarsu duba na tsanaki za ka ga suna da lokacin aikata abubuwa marasa amfani ko wanda ba su kai wannan abun da su ƙi yin amfani ba, yaudarar kansu kawai su ke yi da su ke ganin rashin lokaci ne ya hana su yin abun da ya kamata.
Marubuci: Anas Darazo
Zai ma ka wahala ci-gaba matuƙar ka ci-gaba da amfani da lokacin ka wajen shashanci amma kana cewa ba ka da lokaci idan an zo abu mai amfani.
2. Isasshen lokaci
Tunanin gaba za su samu isasshen lokaci da za su yi abun da ya kamata. Eyyah! Ɗan uwa yanzu ne ka ke da dama, gobe da nisa.
Duk matashin da ya jinkirta taimakon iyaye, neman kuɗi da neman ilimi, inganta lafiya da ƙulla alaƙa mai kyau da mutane ya na ganin sai ya gama jami'a ko sai ya yi aure ko ya yi kuɗi ko sai ya shekara kaza ko ya mallaki abu kaza lallai ya sani shi makararre ne.
Ka yi amfani da damar da Allah Ya ba ka yanzu, ka yi duk abun da za ka iya koda kaɗan ne hakan ka iya zama silar ka ta zama mai nasara, jinkiri kuwa koda na daga safe zuwa dare ne zai iya zama sanadin tabbatar ka cikin ƙasƙanci.
3. Alhakin matsaloli
Ɗorawa wasu mutane alhakin matsalolin da ka ke ciki, matasa da yawa su na ganin matsala ta same su ne sakamakon sakacin wasu mutane kamar iyaye, dangi, shugabanni, iyayen gida ko abokansu, lallai ka sani duk abun da ya same ka kai ya samu babu ruwan wani, idan har ka yi hankalin da ka gane mahaifanka ba su sauke ma ka wani haƙƙi ba wanda hakan ya jefa ka a matsala to ya kamata wannan hankalin naka ya gano ma ka mafita.
Ka sani ba ka da iko akan kowa amma kana da iko akan kanka, don haka manta da wanda sakaci ko muguntarsu ya jefa ka a matsala ba za ka iya tilasta su gyara ba, amma kana da iko da kanka don haka tilasta ma kanka ka yi abun da ya kamata.