Sallama da fatan buɗewar ƙofofin farin ciki da nishaɗi gare ki, tare da farin ciki mai kima da daraja ga ɗiyar girma da daraja a wajena.
Marubuci:- Sadik Ebra
Ɓoyayyen sirri ne zan bayyana gare ki, saboda nazarin da na yi da kuma shawarwarin da na samu a kanki.
Dukkan bishiyoyi da tsuntsaye tare da ruwan sama, duk Allah ya halicce su ne don su zama jin daɗi ga rayuwar Ɗan Adam, numfashi da lafiya duk ba a sayensu saboda sun zama dole ga rayuwa, haka ita ma soyayyar gaskiya ba a sayenta baiwa ce daga Allah.
Yanzu idan na sanar da ke cewa kin ɗauki kaso mafi tsoka wajen sanya ni farin ciki ya za ki ji?
A duk sa'adda muka haɗu koda a hanya ne kwarjininki kan bugi zuciyata, ta yadda ban iya haɗa idanuwana da naki.
Sau da yawa sai na ji murmushi ya cika fuskata a duk lokacin da nake tuno ki, me ya sa hakan?
Ni dai na san a kullum ina yaban halayenki, musamman sanin girman mutane da kulawa da su, amma idan na ce a yanzu haka sunan ki ne na fi yayi da yawan ambato a zuciyata ya za ki ji?
Ki ba ni maganin damuwata ma'ana ki mallaka mini zuciyarki, hakan kaɗai zai kawo waraka gare ni.