Kada hankalin ka ya tashi, don ka ga babbar yarinya, mata sauƙin kai gare su.
Bari ka ɗan ji sirrin su. Farko dai ka daure ka tsala wankan sugar, ka watsa lumtsumeman turarenka mai daɗin ƙamshi, kar ka ji tsoro ka tunkare ta koda a kan hanya take.
Marubuci:- Abubakar Usman
Cikin taushin murya za ka ce mata barka.
Kar ka jira sai ta amsa, kawai ka ci gaba da cewa ki yi haƙuri na san babban zunubi ne a wajen mahukunta idan aka tsaida mace mai aji tamkar ki akan hanya, amma ni ma dole ne ya sa na tsayar da ke, saboda zuciyata ta raya mini cewa wata ƙla idan na bari kika wuce ba za mu ƙara haɗuwa ba, ga shi na daɗe ina son furta miki saƙon ki da aka ba ni a cikin mafarkina mai tsantsar rikitarwa da al'ajabi.
Sai ka ɗan yi shiru ka ji me za ta ce, sannan sai ka ƙara da cewa yanzu me zai hana ki faɗa mini sunan ki da lambar ki, kin ga idan kin koma gida sai na kira ki na faɗa miki saƙon, saboda ina kishin duk wanda ya zo giftawa anan sai ya ga kyakkyawar kwalliyarki, idan kuma ba za ki damu ba sai na faɗa miki yanzu.
Cikin risinawa sai ka ce mata na gode.
Sai ka ɗan yi murmushin isar da saƙo a lokacin da kuka haɗa ido.