Monday, 17 February 2025

Abubuwa 10 Masu Janyowa Mutum Raini

Tura Wannan Zuwa Ga

Waɗannan su ne abubuwa 10 da suke tarwatsa girma da darajar mutum kowa ya raina shi.


Abubuwa 10 Masu Janyowa Mutum Raini
Hoto: Manari TV/YouTube

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Ga su kamar haka:


1. Yawan kule-kulen 'yammata ga namiji


Yawan nuna soyayya ga kowacce mace idan ka gani shikenan ta zama budurwarka, hakan yana sa wa mutuncin mutum ya zube kamar an zuba ruwa a kwando.


2. Yawan yin gulma


Mutanen da ke yawan gulma da yayata magana ba tare da tabbaci ba ana raina su. Nazarin Journal of Social Psychology ya nuna cewa yawan gulma yana rage daraja da amincewa.


3. Rashin iya sarrafa fushi ko matsala


Mutane suna raina wanda ba zai iya sarrafa fushinsa ba ko wanda ke yawan tsawwala magana a lokacin da yake cikin matsala ko yawan mita da ƙorafi.


Nazarin Journal of Emotional Intelligence ya nuna cewa iya sarrafa fushi yana ƙarfafa mutum.


4. Rashin alƙibla da rashin faɗin gaskiya a rayuwa


Idan mutum ba shi da tsayayyen shiri ko burin rayuwa, mutane kan raina shi. 


Nazarin Journal of Career Development ya nuna cewa mutanen da ke da alƙibla sun fi samun mutuntawa a cikin al’umma.


5. Rashin tsaftar jiki da muhalli


Idan mutum ba ya kula da kamanninsa ko tsaftarsa, wasu kan raina shi.


Nazarin Psychology Today ya nuna cewa tsafta tana taka rawa wajen yadda mutane ke kallon darajar mutum.


6. Yawan faɗar sirrin iyalinka ga na waje


Tun da ga kan mahaifi, mahaifiya, matarka, ƙanneka da yayyenka dukkansu fallasa wani asirinsu a waje ga wani kamar kanka ka daɓawa wuƙa ƙarshe idan an tashi har kai za a gorantawa.


7. Rashin dogaro da kai da rashin ƙwarin gwiwa


Idan ya zama ko me za ka yi sai ka nemi shawara ko izinin mutane ko yardar su hakan yana bazar maka da kimarka kamar an watsa gari a iska, don kuwa koyaushe zai zama juya ka ake yi sai abin da aka tsara maka za ka yi ka zama bawan mutane a taƙaice.


8. Yawan tambayar kuɗi ko roƙon taimako


Mutanen da ke yawan roƙon taimako ba tare da ƙoƙarin dogaro da kansu ba, suna zama abin raini.


Nazarin Journal of Economic Behavior & Organization ya nuna cewa mutane suna mutunta waɗanda ke ƙoƙarin magance matsalolinsa.


9. Yawan cewa "Ni ne na fara" ko "Ni na fi kowa"


Mutanen da ke yawan jaddada kansu a kowane yanayi suna sa wasu su raina su. 


Nazarin Personality and Individual Differences Journal ya nuna cewa waɗanda ke da hali na son ɗaukaka kansu ba sa samun mutuntawa.


10. Yawan yi wa wasu kishi da fatan mugun abu


Mutanen da suke yawan jin kishin wasu ko fatan sharrinsu, sukan zama abin raini. 


Nazarin Psychology Today ya nuna cewa kishi da mugun nufi suna rage mutunci a idon jama'a.


Ya ku taron matasa ina horonku da ku guji waɗannan abubuwan.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user