Babban sirrin kasuwa a 2025 shi ne samar da kayayyaki masu sauƙin kuɗi daga abin da muke samarwa a cikin gida. Domestic Market (Production).
Marubuci:- Bello Ado Hussaini
Bincike ya nuna cewa a iya shekarar 2023 kawai, kamfanoni da masu shigo da kaya, sun gaza siyar da kaya na sama da Naira biliyan ɗari uku da hamsin.
Ma'ana ₦350 billion na kaya da ke jibge a sito babu mai siye.
Lissafin kuma ya ci-gaba har cikin shekarar 2024.
Hakan na nuni da sukurkucewar ƙarfin aljihun al'umma, wajen iya sayen kayan amfanin yau da kullum, da na buƙatar rayuwa, wato Purchasing Power.
Waɗannan alƙaluma suna tabbatar da cewa, masu amfani da kaya (Consumers) dole sun haƙura da wasu kayayyakin, sannan kuma sun nemi musayar wasu masu sauƙin kuɗi, Alternative consumer goods.
Wannan tabbas matsala ce ga manyan kanfanoni, a waje ɗaya kuma zai iya zama wata dama (Opportunity) ga ƙananan kamfanoni da masu sana'a.
Tambayar itace; Ta yaya za mu iya cin gajiyar wannan ƙalubale?
Dole ne masu ƙananan masana'antu da 'yan kasuwa su ɗauki damar da take cikin abubuwa guda 3, abin da ake kira Leveraging.
Ma'ana su shigar da waɗannan abubuwa cikin sabon fasali a ayyukan su, yadda kayan da suke samarwa, za su ƙara inganci, tare da rage kuɗaɗen da suke kashewa wajen samar da kayan, da kuma yin amfani da taƙaitaccen lokaci a hannu guda.
Waɗannan abubuwa su ne;
Fasaha
Dole ne masu son cin wannan gajiya, su yi amfani da fasahar zamani, wajen inganta ayyukan su.
Wannan ya haɗa da kayan aiki na zamani masu saukin kuɗi, Machine and Tools, da kuma fasahar kwaikwayo wato Artificial intelligence.
Makamashi
Kowa yasan tasirin makamashi wajen tafiyar da ayyukan masana'antu da masu sana'ar hannu.
Haka kuma kowa na sane da yadda farashin makamashin da aka saba amfani da shi (Conventional Energy) yake tashi sama, daga farashin wutar lantarki zuwa na man Diesal da fetur da iskar gas.
Dole ne mu samo wata hanya mafi sauƙi da arha, kamar Renewable energy irinsu hasken rana (Solar) Sharar gona da ta kamfanonin sinadarai, inda za'a ƙona kamar buntun shinkafa, ƙonannen baƙin mai, domin samar da tururi zuwa makamashi (Black furnace) cikin sauƙi.
Hanya
Ya zama wajibi mu samo hanyoyi masu nagarta, na tafiyar da ayyukan mu cikin tsari da gwaninta da ilimi, yadda za mu horar da ma'aikatan mu, da mu kanmu wajen gudanarwa, yadda za mu taƙaita ta'adi (Waste) da ɓata lokaci (Time management).
Hakan zai haɓaka yawan kayan da muke samarwa, cikin gajeren lokaci, da kuma ingancin kayan.
Wannan kuma shi zai ba wa masu dillancin kaya (Whole sellers) ƙwarin gwiwa, cewa za su iya dogara da kayan gida ba tare da yankewa ba, wato Supply Chain Management.
Ƙaruwar abokan hulɗa kuma, zai iya magance matsalar ƙarancin jari.
Dalili idan ka inganta ayyukan ka, za ka samu waɗanda za su saka order, ma'ana su zuba kuɗi su jira kaya.
Hakan zai ba ka damar yin amfani da dabarar nan ta (OPM). Other people's money.