Ba ni aron hankalin ka, ɗana, rayuwa sai ta ba ka wahala take ɗaga ka sama, idan ka maida hankali kan ita wahalar da baƙin ciki kaɗai za ka tsira, idan kuma ka maida hankali kan darusan sai ka ga da wuri ka ci nasara.
Ɗaukakar da kake nema
Hoto: T Turovska/Istock photo
Marubuci:- Abdullahi Madachi
Ɗaukakar da kake nema tana nan cikin wannan aikin da ka ƙi farawa saboda ganin yana da wahala. Ka fara!
Daga yau ka daina faɗawa mutane abun da za kai gobe kawai gobe su ga ka yi abun. Na lura "Kifin da ya kame bakin sa cikin ruwa, ƙugiya ba ta kamo shi".