Kin cancanci dukkan wani matakin so wanda zuciyoyin masoya suke ba wa abokan junansu a dalilin so da ƙauna. Son ki ya yi nisan zango a cikin raina, dukkan wani tanadin farin cikina ke zan mallakawa.
Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR
Mafi shaharar lokutan da na fi shahara cikin shauƙi suna zuwa ne da shauƙi cikin lokacin da na samu saƙon son ki.
Mazauni da na zauna domin tattalin rayuwar soyayyarki ya zama na musamman cikin irin hikimomi da abubuwan da zuciyata ta tanada musamman domin ki.
Na yi matuƙar sa'a da kuma dacewa cikin ranakun da ke tuna min harafin sunanki.
Assalamu alaiki saƙon gaisuwar amincin so mai fitowa cikin rubutun ƙauna wanda suka taho musamman domin su yi gaisuwa a gare ki.
Kin shiga cikin tsakiyar ruhin zuciyata da tsayuwar neman kasancewa da ke nake kwana.
Kyakkyawar sarauniya murmushinki ya mallaki zuciyata da gangar jikina. Lallai ke sarauniya ce mai cikakken iko. Ina matuƙar son ki.
Ba ni da sauran wata matsala. Sannan na kan kasance cikin tsananin farin ciki a lokacin da na ji an ambaci sunanki.