1. Akan lokaci
Mutunta lokacin wasu kamar mutunta lokacin ka ne, ka yarda da ni idan na ce maka babu abun da yake zubar da kimar mutum kamar a taru a wani waje a ce kai kaɗai ake jira kuma ka ƙi zuwa akan lokaci.
Marubuci:- Abubakar S. Wali
Wani mai hikima ya taɓa cewa har ya fi mutunci da dattaku ka yi saurin zuwa waje da awa ɗaya akan ka zo a makare da minti ɗaya. Zuwa waje akan lokaci alama ce ta ka girmama mutanen da ka je wajen saboda su.
2. Kiran asalin suna
Ka dinga kiran mutane da sunan su na yanka. Idan kana mu'amala da wanda ba ka san sunan sa ba ka tambaya a faɗa maka, ko ka tambaye shi ya faɗa maka da kansa, hakan ya fi ka dinga kiran mutum da Yellow ko Oga ko Malam ko Dogo da sauran su.
Idan har za ka kira mutane da wani inkiya ko laƙabi ya zama saboda girmamawa ne ko raha ba wai saboda ba ka san sunan su ba. Kiran mutum da sunansa na yanka yana sa wa mutum ya ji an daraja shi kuma an mutunta shi.
3. Yanayi mai kyau
Hali da ɗabi'a nagari jari ne, za su maka rana ta inda ba ka taɓa zata ba. Ka girmama mutane kuma ka kiyaye haƙƙin su duk ƙanƙantar sa.
4. Zama abin sha'awa
Ka koyi sauraron mutane fiye da yadda kai za ka so a saurareka, idan wani ya yi wani abu da ya burge ka ka faɗa masa.
Ka zamo mutum mai ɗaga darajar mutane a cikin mu'amala ta hanyar nuna sha'awa a cikin rayuwar su.
5. Rauni
Zai iya yiwuwa abun da kake ɓoyewa mutane saboda kada su ga raunin ka ko kasawar ka ya sa su yi mamakin irin ƙoƙarin ka ko jarumtar ka.
Kada ka ji tsoron nunawa ko faɗawa duniya gaskiya game da kai koda kuwa kana ganin kamar wannan gaskiyar raunin ka ce.
Wane ne kai, daga ina kake shi ne abun da ya bambanta ka da miliyoyin mutane.
Wannan abun kuma ƙarfi ne a wajen ka ba rauni ba. A duk inda ka samu dama a rayuwa ka fitowa mutane a mutum (a yadda kake).