Saturday, 8 February 2025

Irin Tunanin Da Zai Sa Ku Mutu A Talakawa

Tura Wannan Zuwa Ga

Yarda da cewa wani ne ko kai da kanka ne silar zama a talaucin ka, kake tunanin talaucin ka yana da alaƙa da samuwar wani ko rashin samuwar wani a cikin rayuwar ka, ko kake tunanin talaucin ka laifin ka ne, akwai matsala a tare da kai ko ka dinga jin rashin sa'a ko talaucin kansa a jinin ka yake.


Irin Tunanin Da Zai Sa Ku Mutu A Talakawa
Hoto: Pexels

Marubuci:- Abubakar S. Wali


Yarda da cewa an halicce ka ne talaka, ko jin cewa Ubangiji ne yake so ya gan ka a haka (cikin talaucin) har ka dinga tunanin kamar akwai wata falala a cikin talaucin da kake yi.


Yarda da cewa muhallin ka ko wani al'amari da ba a ƙarƙashin ikon ka yake ba shi ne ya tilasta maka zama a cikin talauci, kake ganin kamar babu wani abu da za ka iya yi ka fitar da kanka daga talauci saboda irin al'ummar da ka samu kanka a ciki.


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user