Sunday, 2 February 2025

Karanta Addu'ar Tashi Daga Majalisi

Tura Wannan Zuwa Ga

A'isha, Allah ya yarda da ita, ta ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, bai taɓa zama a wani majalisi ba, ko ya karanta Alkur'ani, ko ya yi wata sallah face ya cika da waɗannan kalmomi.


سُبْحَانَكَ اَللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ، أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ أَسْتَغْفِرُكَ وَأَتُوبُ إِلَيْكَ.


Subhanakal-lahumma wabihamdik, ashhadu an la ilaha illa ant, astaghfiruka wa-atoobu ilayk.


Addu'ar tashi daga majalisi (Domin neman yafewa ga abin da ya gudana a cikin ikin majalisin)
Hoto: Leo Patrizi/iStock photo

Tsarki ya tabbata a gare Ka, ya Allah, da yabo gare Ka. Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, ina neman gafararka, kuma ina tuba izuwa gare Ka.


Sai A'isha ta ce: Ya Manzon Allah! Na lura cewa ba ka taɓa zama a wani majalisi ba, ko ka yi karatun Alkur'ani, ko ka yi sallah face ka faɗi wannan kalmomi.


Sai ya ce; "Ƙwarai. Duk wanda ya faɗi wani alheri sai waɗannan kalmomi su zama kamar hatimi ne ga alherin da ya aikata, wanda kuma ya faɗi sharri, sai su zama kaffara ne gare shi."

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user