Tuesday, 25 February 2025

Ƙaryar Da Ake Yi Muku Kan Kuɗi

Tura Wannan Zuwa Ga

Wanda duk ya ce kuɗi yana canja halin mutane daga mai kyau zuwa mara kyau shi ne yake jira ya yi kuɗin domin halayen sa marasa kyau su ƙara fitowa fili.


Ƙaryar Da Ake Yi Muku Kan Kuɗi
Hoto: Shutter stock

Marubuci:- Abubakar S. Wali


Wanda duk ya ce kuɗi ba ya iya sayen farin ciki bai ba da su ga mai tsananin buƙatar su ba ne.


Wanda duk ya ce kuɗi mabuɗin sharri ne ya fifita neman su ne akan komai.


Wanda duk ya ce kuɗi bai ba shi kima da mutunci ba ƙoƙarin sayen kima da mutuncin yake yi da kuɗi.


Wanda duk ya ce kuɗi ba sa kawo nutsuwa ba ya samun su ta hanya mai kyau ne.


Wanda duk ya ce kuɗi yana kawo wahala a rayuwar mutum shi ne ba shi da godiyar Allah a cikin neman kuɗin sa.


Wanda ya ce kuɗi ba su da muhimmanci a rayuwa shi yake ƙarar da lokacin sa, ƙarfin sa da lafiyar sa a wajen neman su.


Riƙo da waɗannan abubuwan za su iya ba ka matsala wajen neman kuɗin ka.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user