Duk wanda ka gani a wani mataki na nasara, akwai matakin da ya fara wanda ba abun burgewa ba ne.
Marubuci:- Bello Ado Hussaini
Sai dai wannan matakin nasa, wanda mai yiwuwa shi ma wasu masu ƙarancin tunani, sun raina matsayin sa a wancan lokaci, shi ne sanadiyyar samun ɗaukakar sa a yau.
Matasa da dama suna ƙin shiga wasu sana'o'i saboda al'umma ta raina masu wannan sana'ar ba tare da wani dalili ba.
Kuma da yawan irin waɗannan sana'o'in za ka tarar abin da ake samu cikinsu, ya fi na mai matsakaicin albashi.
Wasu kuma sukan ɓoye irin sana'ar da suke gabatarwa, saboda gudun raini ko kallon wulaƙanci.
Babbar illar hakan shi ne, ba za ka sami damar ba wa sana'ar taka irin kulawar da ya kamata ba, tunda a ɓoye kake yin ta.
Abin da ya kamata ka sani shi ne, maula da roƙo da zama cikin talauci, su ne abin jin kunya, amma ba ƙaramar sana'a ba.
Alh. Mustapha Ado mai kamfanin AMMASCO OIL, ya fara da siyar da baƙin mai a galan, yau shi ne mai kamfanin Lubricant ɗan ƙasa mafi girma a Nigeria.
Alh Auwalu Abdullahi Rano, A.A Rano, ya fara siyar da kalanzir a garewani (Drum) abin da ake kira da Ɓunɓurutu/Bunburutu, yau kamfanin sa na A.A Rano Nig Ltd yana cikin kamfanonin da suke ɗaukar Crude Oil a Nigeria, baya ga gidajen siyar da fetur sama da 120, da kuma motocin ɗaukar mai sama da 600.
Kai kanka da kake karanta wannan rubutun, ba za ka rasa wasu misalai da suka faru da wasu da ka sani ba, waɗanda su ma an raina sana'ar da suke yi a baya, kuma yau sun zama abin sha'awa da kwatance a cikin al'umma.
Kowacce irin sana'a kake yi, matuƙar halal ce, ka gabatar da abar ka cikin alfahari da godewa Allah.
Elon musk ya ce "Kada ka ji kunyar sana'ar da kake yi komai ƙanƙantar ta. Kada ka sauya manufar neman ka, saboda wani yana kallon ka a maƙasƙanci.".
Kada ka bari wani sakarai ya hana ka gina rayuwar ka, saboda tasa rashin fahimtar da rayuwa.