Wednesday, 12 February 2025

Yadda Za Ku Gane Budurwar Ku Tana Amfani Da Ku Ne Ba Son Ku Take Ba

Tura Wannan Zuwa Ga

Abubuwa biyar daga Psychology wanda indai budurwarka na yi maka su ba son ka take ba kawai tana buƙatar wani abu daga gare ka ne.


Yadda Za Ku Gane Budurwar Ku Tana Amfani Da Ku Ne Ba Son Ku Take Ba
Hoto: Voyagerix/Dreams time

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Ga su kamar haka:


1. Ba ta son ka san asalin halayenta


Idan tana ɓoye maka wasu abubuwa na halayenta ko danginta ko ƙawayenta, ko kuma ba ta so ka san abubuwan da take yi, to akwai yuwuwar tana amfani da kai kawai.


Mace mai son ka da soyayya tana bayyana maka komai da take yi, sannan sai ta bari kowa ya san ka a danginta, ƙawayenta, kai wata ko jinin haƙiƙa take sai ta gaya maka.


2. Ba ta nuna jin daɗin kasancewa da kai sai idan tana buƙatar wani abu


Idan ka lura cewa tana kiranka ko son ganinka ne kawai lokacin da take buƙatar wani abu, amma ba ta damu da kai ba idan komai yana tafiya daidai a rayuwarta, wannan alama ce ta rashin gaskiya a soyayya. Mutum mai son ka zai kula da kai koda bai da  wata buƙata gare ka.


3. Ba ta ba ka hankalinta ko kulawa da kai


Idan ka fuskanci cewa ba ta damu da matsalolinka, damuwarka, ko burinka ba, wannan yana nuna cewa ba ta son ka da gaske. Wani bincike na psychology ya nuna cewa mutanen da ke ƙaunar juna suna ƙoƙarin fahimtar junansu, da son sanin me ne junansu suke aikatawa. Macen da ke ƙaunar namiji da gaske tana tsananin taya shi jan girmansa, mutuncinsa da kuma son ganin burikansa sun cika.


Idan mace ba ta maka ƙorafi akan ka gyara kurakuranka musamman wanda mutane za su iya rainaka a kansu ko mutuncinka zai zube gaskiya ba ta ƙaunarka.


4. Ba ta da sha’awar samun lokaci da kai ko tattaunawa da kai


Idan mace ba ta damu da samun lokacin tattaunawa da kai ba, sai dai idan tana buƙatar wani abu, to tana amfani da kai ne ba son ka take ba. 


Wani bincike ya nuna cewa idan mutum yana son wani, zai yi ƙoƙarin samun lokaci tare da shi ba tare da wani dalili ba. Macen da ke son ka kowacce doka za ta karya don ta samu ku tattauna da ita.


5. Tana yawan tambayarka buƙatunta kamar kuɗi ko wata alfarma amma ita ba ta taɓa hoɓbasa wajen ganin ta kyautata maka da kyauta koda ta abinci ce.


Idan mace kullum tana buƙatar taimako daga gare ka, kuɗi, lokaci, goyon baya amma ba ta ƙoƙarin taimaka maka da komai a zamantakewarku, wannan yana nuna tana amfani da kai ne kawai.


Masana psychology suna cewa soyayya tana buƙatar bayarwa da karɓa (reciprocity), ba wai mayar da mutum ɗaya ya zama kamar bawa ba.


Idan ka ga saɓanin haka kuma ka ci gaba da soyayya da ita gaskiya laifin ka ne.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user