'Yanci
Kada ka zamo mai tsatstsauran ra'ayi akan wani al'amari, tunani, aƙida ko fahimtar da za ta sa ka ɗauki mataki ko yin aikin da zai cutar da kai ko wani, domin kawai ka kare wannan aƙidar, al'amarin ko tunanin.
Marubuci:- Abubakar S. Wali
Idan ka ba wa kowa 'yancin yin rayuwa yadda yake so kamar ka ba wa kanka wannan 'yancin ne.
Mafita
Ka zamo mai buɗaɗɗen tunani a kowane lokaci, ka yarda za ka iya kuskure akan wata fahimta ko tunani, ka zamo ɗalibin rayuwa na din-din-din.
Ɓoyewa
Wannan yana da matuƙar muhimmanci a cikin zaman ka lafiya a rayuwa, ya zama ba ka da wani abu ko wata rayuwa da kake ɓoyewa ba ka so mutane su sani.
Mafita
Idan akwai wani abu da kake yi da kake jin tsoron mutane su sani to ka daina yin wannan abun da gaggawa.
Ka daina ɓoye wane ne kai ko asalin ka ko daga wajen da ka fito, ka daina jin kunyar daga ina kake ko a ina kake yanzu, abu mafi muhimmanci a cikin rayuwar ka shi ne wajen da ka nufa.
Maslaha
Ka yi ƙoƙarin cire son zuciya a duk cikin al'amuran ka na rayuwa, kar ya zama kullum maslahar kanka kake fara kallo.
Mafita
Ka zamo adali a tunani a ɗabi'a a hukunci da kuma a mu'amala.
Farmaki
Ya zama a rayuwa ba ka da abokin faɗan da za ka kai wa farmaƙi walau mutum ko wani al'amari.
Za a iya samun saɓani na ra'ayi, aƙida, tunani, fahimta da sauran su tsakanin ka da wasu mutane amma kada wannan saɓanin ya jawo ka ɗauki matakin da zai cutar da kai ko wani.
Cutarwar za ta iya kasancewa ta ruhi ko ta jiki ko ta tunani, duka cutuwa ce.
Mafita
Ka karɓi mutane a yadda suke ba tare da ƙoƙarin canja su ba.