Wednesday, 5 February 2025

Zazzafar Wasikar Rabuwa Da Budurwa Mai Ratsa Zuciya Sosai

Tura Wannan Zuwa Ga
Zuwa ga Budurwata a da.

Ina fatan wannan wasiƙar ta same ki cikin ƙoshin lafiya da jin daɗi. Na zauna domin rubuta wannan wasikar ne don na bayyana yadda rayuwar mu ta kasance, labarin zahiri da ke fitowa daga zuciyata. Ina fatan rabuwar mu za ta samar da kyakkyawar fahimta da sabuwar dama ga kowannen mu.

Zazzafar Wasikar Rabuwa Da Budurwa Mai Ratsa Zuciya Sosai
Hoto: Konstantin32/iStock photo

Marubuci:- Musa Madaki

Rayuwar mu tare ta kasance cikin yanayin matsanancin farin ciki a wasu lokutan, dariya a wasu lokutan, hawaye a lokacin da alaƙar ta ƙuntata, mun haye tsaunuka tare haka mun ratsa teku mai haske da mafi duhu a tare, haƙiƙa annashuwa da kyakkyawan mafarkin rayuwa da juna ya wanzu a rayuwar mu da mafarkin mu, mun sadaukar da kawunanmu ga junanmu don tabbatar da annashuwa a zamantakwar mu, duk da haka na zo na tabbatar da rabuwar hanyar rayuwarmu abun da ya sauya alƙiblar mu.


Rabuwar mu matsaya ce mai cike da raɗaɗi wacce  kuma ba ta da makawa, kuma za ta kasance jimami mai girma a ciki rayuwata, wannan matsayar ba ta kasance cikin farin ciki ba kuma ba za ta taɓa zaɓa abun da na so ba, dukkanmu ni da ke muna buƙatar mu rayu cikin farin ciki da cikakkiyar walwala, kasancewar mu tare ƙalubale ne ga samuwar hakan. 


Bayan waƙi'ar rabuwar mu, zan yi amfani da dukkan darasin da tarayyar mu ta koyar da ni da kuma damar samun ci-gaba da na samu, kowacce tarayya tana da babban abun duba da na koyi a cikinta haka tamu ita ma ba ta sha bamban ba. Ina godiya da lokutan farin ciki da nishaɗi da muka kasance tare da kuma ƙalubalen da muka fuskanta a zaman mu wanda suka samar da mutum kama ta a yau. 


Rabuwa da matsawa gaba don ci-gaba da sabuwar rayuwa. Ina fatan hakan zai zama babbar damar samun farin ciki da cikar burin da kowannen mu ke nema, da tabbatar da mafarkin kowannen mu. Ya zama dole ni da ke mu ɗauki rabuwar mu a matsayin babbar dama ta nemo sahihiyar hanyar da ta fi dacewa da mu.


Ina son miƙa jinjina ta ga lokutan da muka shafe tare da darasin da hakan ya koyar da mu, waɗannan lokutan za su ci-gaba da zama abubuwan tunawa a cikin rayuwata wanda ba za su taɓa gushewa ba a zuciya ta har abada.


Babu abun da nake miki fata a cikin rayuwarki face kasancewa cikin alkhairi na har abada. 


Allah ya ba ki farin ciki da cikar buri da soyayyar da ta dace da ke. 


Ki kula da kanki.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user