Kana buƙatar fiye da aiki tuƙuru a wajen neman nasara. Ba rayuwar ba ce me wahala, zaton rayuwar ta zo maka da sauƙi shi ne wahalar.
Marubuci:- Abubakar S. Wali
Ka yarda da ni idan na ce maka kana buƙatar aiki tuƙuru a duk wani fanni na rayuwar ka da kake neman samun ci gaba ko nasara a cikin sa, amma mafi yawan lokaci aikin ka yana buƙatar fiye da zallar aiki kafin ya ba ka sakamakon da kake buƙata.
Kana buƙatar hangen nesa.
Za ka yi mamaki idan na ce maka mutane da yawa aiki ba dare ba rana har ya fi musu sauƙi akan zama na wani lokaci su kalli ina rayuwar su ta sa gaba, a ina suke da matsala, ya za a yi su magance ta, a ina za su iya samun matsala? Ta wacce hanya za su iya hana faruwar ta? Wane irin sakamako rayuwar su ko aikin su na yau zai iya haifarwa a rayuwar su ta gobe.
Matsalar shi ne mutane sun fi kambama tasirin aiki tuƙuru a cikin rayuwa fiye da tasirin tunani mai kyau a cikin rayuwar.
Dukkanmu muna aiki tuƙuru a wani ɓangare na rayuwarmu, kodai mu yi aiki tuƙuru wajen warware matsala ko mu yi aiki tuƙuru wajen haddasa matsalar.
Hatta malalaci mai gudun aiki tuƙuru yana aiki tuƙuru wajen gujewa aiki tuƙurun.
A taƙaice abun da ya fi wahala shi ne tunani, shi yasa mutane da yawa ba sa iya yin sa, hanyar bambanta kanka da mafi yawan mutane shi ne ka haɗa aiki tuƙurun ka da hangen nesa, yadda ba ka yi kasala da jikin ka ba haka kada ka yi kasala da ƙwaƙwalwar ka wajen yin tunanin da zai inganta rayuwar ka.
Ka yi tunani domin ka san wane ne kai, ka yi tunani domin ka yi rayuwa da manufa.