Monday, 10 March 2025

Abubuwa 10 Masu Amfanarwa

Tura Wannan Zuwa Ga

1. Sanin cewa duk mutum na da matsalolinsa


"Illusion of Transparency" yana nuna cewa kowa yana jin kamar matsalolinsa sun fi yawa, amma a gaskiya kowa yana da matsala kuma kowa tasa ya sani (Gilovich et al., 1998).


Gaskiya 10 Masu Amfanarwa
Hoto: Your Tango

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


2. Kamanta rayuwarka da ta shafukan sada zumunta


Nazarin Self-Discrepancy Theory ya nuna cewa yawan kallon rayuwar wasu a shafukan sada zumunta da ƙoƙarin kwatanta abin da suke yana karya lagon mutum da mayar da shi baya (Higgins, 1987).


Bincike ya nuna cewa wanda suka fi amfani da shafukan sada zumunta kaso 70 cikinsu suna fama da cutar "Depressions "wato  cutar damuwa. 


Kawai suna ta ƙoƙarin neman abin da zai ɗebe musu kewa ne.


3. Ƙwarewa akan neman kuɗi fiye da tara su waje ɗaya


Bincike ya nuna cewa mutanen da ke saka kuɗinsu a ƙwarewa (kamar tafiya ko koyon sabuwar sana’a) sukan fi jin daɗi fiye da masu ajiye kuɗin kawai ba sa ƙoƙarin zuba kuɗin inda za su haɓaka.(Van Boven & Gilovich, 2003).


4. Sanin cewa ba kowa zai so ka ba


"Negativity Bias " yana nuna cewa mutane kan fi mayar da hankali ga rashin so fiye da soyayya, mutane sukan fi damuwa da maƙiyansu akan masoyansu.


Misali , Ɗan Siyasa zai fi damuwa da ya jawo maƙiyansa su dawo masoyansa, haka budurwa ba ta cika damuwa da namijin da yake nuna mata tsantsar soyayya ba, tana ta ƙoƙarin cusa kai wajen namijin da bai damu da ita ba. 


Dalilin haka kuma kaso 90 suke rasa masoyan nasu wajen neman soyayyar wasu da ba su damu da su ba. Ɗan siyasa ya kan rasa masoyansa wajen ƙoƙarin kyautatawa abokan adawarsa ya manta da hidima wa masoyansa. 


Haka ita ma macen ke rasa masoyi na gaske wajen ƙoƙarin shawo kan wanda bai damu da ita ba (Baumeister et al., 2001).


5. Sanin lokacin da ya dace ka yi magana da wanda za ka yi shiru


Emotional Intelligence yana nuna cewa sanin lokacin yin shiru da lokacin magana yana ƙarfafa dangantaka da mutanen da ke kewaye da kai (Goleman, 1995).


Ba komai ne sai ka sa baki akai ba koda kuwa kana da iko ko akan 'ya'yan cikinka ne.


6. Guje wa rashin haƙuri da son komai a gaggauce


Delayed Gratification yana nuna cewa mutane masu iya jira don samun sakamako mai kyau sukan fi samun nasara (Mischel et al., 1972).


7. Yin godiya da abin da kake da shi


Nazarin Positive Psychology ya tabbatar da cewa mutanen da ke yin godiya akai-akai sukan fi samun kwanciyar hankali (Emmons & McCullough, 2003).


8. Sanin cewa lokaci shi ne abu mafi daraja


Mutanen da suka fahimci cewa lokaci ba ya dawowa sukan fi amfani da shi cikin hikima (Carstensen et al., 1999).


9. Guje wa yin buri ba tare da aiki ba


Fantasy Realization Theory ta nuna cewa mutane da ke yin tunanin nasara ba tare da aiki ba, suna fuskantar gazawa (Oettingen, 2014).


Ka yi aiki da hankali da basira kada ka zama mai son cin banza da neman alfarma akan komai.


10. Sanin cewa rayuwa na buƙatar Daidaituwa


Work-Life Balance Theory ta tabbatar da cewa mutane da ke daidaita aikin su da rayuwarsu sukan fi farin ciki (Greenhaus & Allen, 2011).

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user