Ƙarya ita ce dukkan wani bayani da aka ɓoye gaskiyar sa, aka ambaci ambaci saɓanin daidai da nufin a cutar da wanda ake isar wa bayanin.
Abubuwan Da Ake Ɓoye Muku Kan Ƙarya
Hoto: Penn State
Marubuci: Taska
Ga ingantanttun misalai 3:
1. Kamar wani ya ga ka sayo wani abu na kayan abinci ko kayan amfani, sai ya zo yana tambaya nawa ka saya, don ƙila shi ma ya sayo irinsa, ko don idan ya je saye kar a cuce sa, sai ka faɗa masa saɓanin abin da ka sayo, ko dai don kar ya je ya saya, ko kuma don idan ya je, ya raina kansa.
2. Kamar wani ya tambayeka ya zai yi abu kaza, ko ya za a yi ya je wuri kaza, sai ka faɗa masa saɓanin gaskiya da gangan.
3. Kamar a zo ana neman warware wata matsala da kai ka san haƙiƙanin abin da ya faru, amma ka faɗi saɓanin haka. Kamar an yi sata a idonka, ko an zalunci wani a idonka, sai a nemi ka faɗi gaskiya sai ka faɗi saɓanin gaskiyar.
Amma ƙarya da mata da miji suke yi wa juna, kamar; ta yi girki bai yi daɗi ba, amma saboda kar ta damu kanta sai ka ce mata ya yi daɗi.
Ko mutane su yabi junansu don su saka wa kansu farinciki, kamar ƙaryar da tafi shahara da ake cewa Kano koda me ka zo an fi ka.
Irin wannan ba a kiransa ƙarya, saboda babu wanda zai cutu daga faɗin hakan.
Ƙaryar da a ka yi ta bisa binciken ilimi amma sai a ka yi rashin sa'a ba haka haƙiƙanin abin yake ba, ba a kiransa ƙarya sai dai a kirasa kuskuren fahimta ko iitiƙadi da abinda yake ba daidai ba, ko saɓanin fahimta ko wani abu makamancin haka.
- Kamar mutum ya riƙa yaɗa cewa duniya shimfidaddiya ce ba dunkulalliya ba.
- Ko ruwa daga wani wuri yake zubowa ba wai daga ƙasa yake tashi ya taru a sama ba sannan ya dawo ƙasa.
- Ko tunanin akwai aljannu da za su iya shiga jikin mutum kuma su yi tasiri.
-Ko tunanin ɗan adam ya samo asali daga kaza.
- Ko tarihin gari kaza, kaza ne.
Duk ƙaryar da ba a yi ta da nufin cutarwa ba, ba a kiranta da haƙiƙanin ƙarya.