Wednesday, 26 March 2025

Alamomi 10 Na Zama Mahaukaci

Tura Wannan Zuwa Ga

Wadannan su  ne abubuwa 10 da ke nuni da saura kaɗan ka zama cikakken mahaukaci. Idan mutum yana da waɗannan alamomi, yana da kyau a nemi taimakon likitan ƙwaƙwalwa da wuri kafin lamarin ya yi tsanani.


Alamomi 10 Na Zama Mahaukaci
Hoto: skynesher/Getty Images

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Ga su kamar haka:


1. Rikicewar tunani


Tunanin mutum ya rikice ya kasa tantance me zai yi a rayuwa? Ina ya kamata ya dosa ? Me ne ne zai amfane shi?


2. Ganin abubuwa da ba su wanzu ba


Ko yana ɗaki ya dinga ganin giftawar wani abu mai rai ko mara rai, ko ya dinga jin maganganu ko ana kiransa wanda a zahiri gizo ne.


3. Rikicewar hankali


Ya dinga imani da abubuwan da ba su da tushe, kamar cewa ana bibiyar rayuwarsa za'a cutar da shi, ko ya dinga tunanin yana da wata baiwa ta musamman kamar  kusanci da aljanu ko wata halitta ɓoyayyiya.


4. Rashin kulawa da kansa


Ya daina wanka, wanke kaya, ko gyara kansa.


5. Matsananciyar ƙiyayya da mutane


Yana guje wa jama’a ko jin cewa kowa maƙiyinsa ne.


6. Rashin barci ko barci mai yawa


Kodai ba ya samun barci kwata-kwata ko yana yin barci sama da kima.


7. Rashin jin daɗi da rayuwa


Zai iya rasa sha’awar rayuwa ko jin cewa babu amfani a rayuwarsa.


8. Aikata abubuwan da ba su dace ba


Yana son yawo tsirara cikin ɗaki ba ya son saka wando, yana magana da kansa, ko aikata abubuwa masu hatsari ba tare da tunanin hatsarin ba.


9. Rashin gane gaskiya da wuri sai ya aikata abu ya dawo yana da-na-sani


Yana kasa banbance abin da ya kamata wanda zai dace daidai da shekarunsa, ya dinga yin abubuwa da ya kamata a ce wanda suke ƙasan shekarunsa ke aikatawa.


10. Saka sutura wadda ta sha bamban da yanayin da ake ciki


Ya dinga saka ƙatuwar rigar sanyi lokacin zafi, ko kuma ya dinga yawo da singileti lokacin da ake sanyi.


Idan ka ga waɗannan alamomin ina mai yi maka bushara da cewa ka kusa haukacewa.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user