1. Macen da ke lura da ƙananan abubuwa game da kai tana ƙaunarka.
Kamar sabon aski idan ka yi ko idan ka rage gemunka ko sajen ka.
Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint
2. Macen da koyaushe ke ƙoƙarin taimaka maka da ƙananun abubuwa kamar turare ko ba ka kyautar abinci tana da wani motsin soyayya mai ƙarfi a gare ka.
3. Macen da ke tunawa da ƙananan bayanai game da kai tana daraja ka sosai.
Kamar sunan 'yan gidanku, wacce makaranta ka yi? sunan abokanka da sunan iyayenka, wanne abinci ka fi so? Wanne gurin ƙwallo kake so da sauransu dai.
4. Idan mace tana keɓe lokaci domin kai duk da kasancewar tana cikin aiki, tana kula da kai sosai.
Misali duk hayaniyar gidan bikin da take ciki sai ta ware lokaci ta kira ka duk uzurin da take ciki ba ya hana ta mantawa da kiranka.
5. Idan tana kare ka a gaban jama’a amma tana gyara maka kuskure a sirrance.
6. Macen da ke sauraron surutunka ba tare da gundura ba tana ƙaunarka da gaske.
7. Idan tana lura da shirunka kuma ta tambayi abin da ke damunka, tana son ka da gaske.
8. Macen da ke gardama da kai amma ba ta taɓa barin ka ba. Duk yadda za ku yi faɗa ba ta iya share ka na tsawon kwanaki.
Idan ba ka samun wannan daga matarka ko budurwarka lallai ba ta son ka.