Daga lokacin da ka san abun da kake so a rayuwa, kuma ka samu hanyar samun wannan abun, sannan ba ka saɓa doka ba kuma ba ka shiga haƙƙin kowa ba, kawai ka toshe kunne ka ɗauki hanya.
Marubuci:- Abubakar S. Wali
A lokacin da ka ɗaura ɗamarar gyara ko inganta rayuwar ka mutane da yawa ba za su iya fahimtar ka ba, kawai sai dai su ga kana yin abu ko rayuwa daban da yadda suke yi ko daban da yadda suka fahimta shi ne daidai.
Wannan ya sa babu amfani ka ɓata lokaci ko ka yi asarar kuzarin ka wajen dagewa sai mutane sun fahimce ka ko sai sun fahimci ƙudurin ka, alhali da yawa ba za su iya yin hakan ba.
Idan mutane suna mu'amalantar ka kamar ba su fahimce ka ba, kai ma ka mu'amalan ce su kamar ba ka fahimce su ba a cikin rashin fahimtar ka da suka yi.
Ba kowa ne zai iya fahimtar ka ba.