Ka rubuta sunan ka cikin masu hankali, muddin ka daina ɗaurawa kanka buƙatun da suka fi ƙarfin ka.
Marubuci:- Abdulfatah Yakubu
Rayuwa sauƙi gare ta, tuni masu wayau suka daina ɗaurawa kansu abun da ya fi ƙarfin su. Lissafin farko dai shi ne ka rayu, duk wani karatu sai dai ya biyo bayan wannan.
A sauƙaƙe, za mu iya cewa hanyar rayuwa guda biyu ce; akwai mai sauƙi, akwai akasin haka.
Ka natsu ka fahimci wacce ce ta fi dacewa da kai, domin sauƙin wani zai iya zama wahalar wani.
Bahaushe ya ce "abincin wani gubar wani".
Ka fahimci kanka da kyau, ka ci, ka sha, ka yi suturar da ba za ta gigita samun ka ba, ka gina gidan da kula da shi ba zai zame maka ƙarfen ƙafa ba, idan ka tashi aure ka auro mai fahimta irin taka, wacce za ku haɗu ku rufawa kanku da 'ya'yan da za ku haifa asiri.
Rayuwa sauƙi gare ta, idan ka cire bautar Allah babu abun da ya zama wajibi sai abun da bawa ya ɗaurawa kansa.
Hatta Allah idan ya sauƙaƙawa bawa, yana so ya bi wannan sauƙin da ya yi masa.
Ka bi sauƙi, sai ka ga sauƙi.