Monday, 17 March 2025

Daɗaɗan Kalaman Barka Da Shan Ruwa Ga Budurwa

Tura Wannan Zuwa Ga
Ke ɗin rayuwata ce, ke komaina ce, rayuwa ba tare da ke ba, tamkar duniya ce da ta kasance babu hasken rana a cikinta. Ina son ki. Barka da shan ruwa gimbiyata.

Daɗaɗan Kalaman Barka Da Shan Ruwa Ga Budurwa
Hoto: Freepik


Soyayyarki aba ce mai ƙayatarwa da take binne a cikin zuciyata.

Kamar yadda hasken da ke haske sararin samaniya ba zai fassaru ba ta cikin kalmomi, tamkar haka ne zuciya ba za ta iya ƙididdige adadin yadda kumfar soyayyarki ke kaɗawa ba a cikinta. Ina son ki. Fatan kin sha ruwa lafiya abar ƙauna?


Kin samar da wani tabo a cikin zuciyata, wanda ba mai iya jinyarsa face ke. Ke kaɗai ki ka mallaki makullin sarrafa tunanina, ina farin ciki da hakan, saboda babu wata wadda za ta iya kulawa da ni tamkar ke. Ke ɗin sarauniyata ce.

Fatan kin sha ruwa lafiya?

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user