Saturday, 15 March 2025

Daga Wannan Shekara

Tura Wannan Zuwa Ga

Kana matashi daga wannan shekera, ka daina ƙoƙarin burge kowa musamman 'yammatan nan, ka kashewa kanka da burin ka wannan kuɗin za ka ga yadda mutane da 'yammatan za su bibiye ka.


Daga wannan shekara
Hoto: Gatty images

Marubuci:- Abdullahi Madachi 


Inda hali ka gujewa soyayya, idan kuma ka afka ka daina renon ta da naira, soyayyar da aka gina da kuɗi da kuɗi kaɗai ake iya raya wannan soyayya, dan haka kar ka sa kanka a wannan rigima.


Ba wanda zai taimake ka ina tabbatar maka kai za ka tashi ka taimaki kanka, waɗanda suka manta da kai burin su suke ginawa, kai ma ka mantasu ka fuskanci mafarkinka ko burin ka ko muradin ka.


Kar ka sake yi wa wani ƙorafin mai ya sa ya daina damuwa da kai, domin kulawar da ke zuwa bayan ƙorafi wayancewa ce kawai.


Ka yarda da kanka! Zaki bai taɓa damuwa da abin da dabbobin ke cewa akansa, wanda ya yarda da kansa bai damuwa da cecekucen mahassadansa.


Cikar yarda da kanka shi ne yin shiru yayin da ka gano har a zuci ba sa son ka, yin shiru yayinda suke dariya akan mafarkinka, yin shiru yayin da suke gulmarka a gefe suna zaginka.


Indai ba ka manta burin ka ba to kawai ka ci gaba da tafiya kai kaɗanka!

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user