Ke ce halitta mafi kawaici da tarin alkairai da na taɓa haɗuwa da ita. Tabbas na zamo mai sa'a da kasancewar ki a tare da ni a matsayin abokiyar rayuwata.
Na yi miki alƙawarin kasancewa a tare da ke har zuwa ranar fitar numfashina na ƙarshe. Ki yi sahur lafiya.
Shin kina tunanin zan yi tunani kan wani abu da zai amfane ni a rayuwa ba tare da na fara kiran sunanki da farko ba? Ki huta lafiya.
Ke kaɗai na zaɓa, ke kaɗai zan so, na ririta, na yayata, na gabatar da ita a gaban dangina.
Da ke zan rayu, na kasance cikin hidimta miki har na ƙarshen rayuwata. Ina son ki.
Ki yi sahur lafiya.
Allah ya karɓi ibadunmu Amin.